Yanzu Yanzu: Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Osun
- Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Ademola Adeleke ya lashe zaben gwamnan jihar Osun
- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ce ta sanar da sakamakon zaben a safiyar yau Lahadi, 17 ga watan Yuli
- Adeleke dai ya lallasa babban abokin hamayyarsa kuma gwamna mai ci, Gboyega Oyetola, a zaben wanda aka yi a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Osun - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP),Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.
Baturen zabe a jihar, Toyin Ogundipe, ne ya sanar da sakamakon zaben a safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, jaridar The Cable ta rahoto.
Adeleke ya samu kuri’u 403, 371 wajen lallasa babban abokin hamayyarsa Gboyega Oyetola na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya samu kuri’u 375,027.
Dan takarar na PDP ya lashe kananan hukumomi 17 yayin da gwamna mai ci ya samu kananan hukumomi 13 kacal, jaridar Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaben Osun: Ni Zan Ci Zabe, In Ji Oyetola Bayan Ya Kada Kuri'arsa
A baya mun kawo cewa Gboyega Oyetola, gwamnan Jihar Osun, ya ce shi mutane za su sake zaba. Da ya ke magana da manema labarai bayan ya jefa kuri'arsa a ranar Asabar, Oyetola ya ce mutane 'suna sane' kuma sun ga bukatar su fito su yi zaben, The Cable ta rahoto.
Gwamnan ya ce idan har ba a boye-boye a harkar, babu bukatar a rika bi ana cewa mutane su yi zabe. "Zabe na tafiya lafiya kalau.
Yana da kyau a samar da isasun na'ura domon a kammala zaben a cikin lokacin da aka kayyade," in ji shi.
Asali: Legit.ng