Shettima: Yan Najeriya Sun Mayar Da Hankali Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Na Bunkasa Ta Fasaha

Shettima: Yan Najeriya Sun Mayar Da Hankali Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Na Bunkasa Ta Fasaha

  • Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023, Sanata Kashim Shettima ya bukaci yan Najeriya su dena la'akari da addini kadai wurin zaben shugabanni
  • Tsohon gwamnan na Jihar Borno ya ce yan Najeriya sun mayar da hankali kan batun addinin yan takara a yayin da wasu kasashen duniya ke cigaba a bangarorin fasaha da lafiya
  • Shettima ya yi watsi da zargin da wasu ke yi na cewa kasancewarsa da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yan takarar APC barazana ce ga wadanda ba musulmi ba a kasar, yana mai cewa gyaran kasa ke gabansu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Borno - Sanata Kashim Shettima, abokin takarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023 ya ce su dena takaita tunaninsu kan addini yayin zaben shugabanni, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Atiku: Tikitin Musulmi Da Musulmi Yasa Ban Amince Da Tinubu Ba Lokacin Da Yake Son Zama Abokin Takara Na

Zaben Shettima a matsayin mataimakin Tinubu ya janyo suka daga mutane saboda su biyu musulmi ne.

Sanata kashim Shettima
Shettima: Yan Najeriya Sun Mayar Da Hankali Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Na Bunkasa Ta Fasaha. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Da ya ke magana a ranar Juma'a yayin da ya karbi bakuncin tawagar APC karkashin jagorancin Mohammed Hassan, tsohon jakadan Najeriya a Amurka, tsohon gwamnan na Borno ya ce abin da ke gabansa da Tinubu shine sauya kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa Tinubu ba shi da wani niyyar musuluntar da Najeriya.

"Yanzu muna zamani ne na fasaha, a wasu kasashen, mutane suna zancen fasahar nanotechnology, biotechnology da quick data da artificial intelligence, amma muna nan muna magana kan fadar makiyaya da manoma, yan bindiga, garkuwa, yaki da Boko Haram da maganar hadin addini," NAN ta rahoto yana cewa.

Ya cigaba da cewa aikin da ke gabansa shine samar da yanayi na adalci a kasar inda kowa zaiyi amanna ana yi da shi kuma mutane su rika hakuri da juna.

Kara karanta wannan

2023: Ku kwantar da hankali, za fa ku ci zaben nan, Buhari ga Tinubu da Shettima

Ya yi watsi da zargin da ake ma Tinubu na musuluntar da kasar yana mai cewa da gaskiya ne da ya fara daga gidansa.

Ya ce Asiwaju Bola Tinubu musulmi ne amma bai tilastawa yayansa addininsa ba, inda ya ce shine gwamna na farko da ya mika makarantun mission ga masu shi kuma yana daukan nauyin mutane daga kowanne bangare.

A bangarensa, Hassan ya fada wa Shettima cewa ya ziyarce shi ne don sanar da shi game da taron jin ra'ayi da ke tafe inda yan takarar APC za su fada wa mutane tsare-tsaren da suke da shi.

APC Ta Zabi Wanda Zai Maye Gurbin Kashim Shettima a Majalisa

A wani rahoton, Jam'iyyar APC reshen Jihar Borno ta zabi Antoni Janar na Jihar, Kaka Shehu Lawan a matsayin dan takarar kujerar sanata na Borno Central da a halin yanzu Sanata Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ke kai.

Kara karanta wannan

2023: Sabon sabani ya kunno kai a APC kan wanda Tinubu ya zaba mataimaki, Gwamna El-Rufa'i ya fusata

Baturen zabe na jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Uba Magari yayin sanar da sakamakon zaben da aka yi a sakatariyar jam'iyyar a Maiduguri a ranar Alhamis, 14 ga watan Yuli ya ce tsohon kwamishinan shariar ya samu kuri'u 459 cikin 480 masu kyau, rahoton The Sun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164