Kwankwaso: Abin Da Yasa Na Zabi Bishof Idahosa Matsayin Abokin Takara Na
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP mai kayan marmari a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fadi dalilin zaben Idahosa a matsayin mataimakinsa
- Tsohon gwamnan na Kano ya ce cikin mutum 20 nagartattu da ya tace, ya zabi Idahosa ne saboda tsabar amincinsa da ayyuka da kuma fahimtar matsalolin Najeriya da son ganin kawo cigaba a kasar
- Kwankwason har wa yau ya ce Bishop Idahosa mutum ne wanda zai zama abin koyi ga matasan Najeriya yana mai nuna fari cikin ganin ya amince su yi aiki tare
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya ce ya zabi Bishop Isaac Idahosa ya yi masa mataimaki ne saboda tsabar amincinsa, rahoton Vanguard.
Kamfanin Dillancin Labarai Na Kasa, NAN, ta tuno cewa a ranar Alhamis ne aka sanar da Idahosa a matsayin wanda zai yi wa Kwankwaso mataimaki.
Musulmi da Musulmi: Kada ku yarda wani fasto ko limami ya fada maku wanda za ku zaba, Keyamo ga yan Najeriya
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hadimin Kwankwaso a bangaren watsa labarai, Muyiwa Fatosa, ya fitar a ranar Juma'a.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mutane 20 na tankade na zabo Idahosa, Kwankwaso
Kwankwaso ya ce ya zabi Idahosa ne bayan natsatsen nazari da tankade da rairaya daga cikin mutum 20, wanda dukkansu sun cancanta su zama abokan takararsa.
"An zabi Idahosa ne saboda ayyuka masu kyau da ya yi, tsabar amincinsa, da fahimtar Najeriya da kallubalen da ke adabar ta a yanzu."
Kwankwaso ya ce Idahosa mutum ne wanda ya dukufa don ganin cigaban Najeriya kuma ya yi imanin cewa, ana iya samar da sabuwa kuma mafi kyau idan aka rungumi gaskiya, hakuri, cancanta da imani.
"Dan Najeriya na gari kuma wanda ya samu nasarori daban-daban, An zabi Bishop Idahosa ne kuma saboda shi abin koyi ne ga matasan Najeriya," in ji shi.
Kwankwaso ya bayyana farin cikinsa kan cewa mutum mai tsoron Allah zai yi aiki tare da shi domin ceto Najeriya.
Ya ce tawagarsa za ta ceto Najeriya daga kallubalen da ta ke fuskanta tare da kirkirar sabuwar Najeriya inda adalci, daidaito, hadin kai, tsaro da cigaba duk za su inganta.
Kwankwaso: Idan na rasa kujerar Buhari, kowa ma ya rasa, amma Tinubu ya samu
A wani rahoton, Rabiu Kwankwaso ya ce zai marawa takwaransa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu baya, idan ya ga ba zai ka ga gaci ba a zaben 2023.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da yayi a gidan talabijin na Arise a daren Lahadi.
Tsohon gwamnan na Kano ya yi magana ne biyo bayan sanarwar da Tinubu ya yi na zabi Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa.
Asali: Legit.ng