INEC ta kammala shirin zaben da za a gudanar a jihar Osun

INEC ta kammala shirin zaben da za a gudanar a jihar Osun

  • Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta ce ta kammala shirinta tsaf na gudanar da zaben gwamna da za ayi a jihar Osun
  • Kwamishinan INEC na Jihar Osun ya ce ba aikin su bane hana saye da siyar da kur'iu a lokacin gudanar da zabe
  • INEC ta kammala raba muhimman kayayyakin gudanar da zabe a duka kananan hukumomi 30 na jihar Osun

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Osun - Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta INEC, ta ce ta kammala duk wani shirye-shiryen da zata yi dan gudanar da zaben jihar Osun a ranar Asabar 14 ga watan Yuni. Rahoton BBC

Hukumar zaben ta ce tayi hakan dan gujewa matsaloli a ranar gudanar da zaben

INEC, ta ce yayin da ya rage lokaci kadan a fara kada kuri’a a fadin jihar, tuni ta rarraba takardun zabe ga kananan hukumomin jihar 30.

Kara karanta wannan

Zaben Osun : Ba Aikinmu Bane mu hana saye da Siyar da Kuri'u, Inji Kwamishinan INEC

INECI
INEC ta kammala shirin zaben da za gudanar a jihar Osun FOTO VANGUARD
Asali: Twitter

Hukumar INEC ta ce a gaban jam’ian tsaro aka rarraba kayayyakin gudanar da zabe masu muhimmanci

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Cikin masu sa ido akan harkan zabe na hukumar INEC, Hajia Zainab Aminu ta je Osogbo dan ganin yadda abubuwa ke wakana, kuma ta shaidawa manema labaran BBC cewa INEC ta yi nasarar rarraba muhimman kayayyakin zabe a wurare daban-daban a jihar.

Sai da ta ce Hukumar ta INEC, ta fara aikewa da kayan zaben ga kananan hukumomin da ke da nesa dan isa da wuri sannan aka rabawa na kusa, zuwa gundumomi daga nan kuma sai rumfunar Zabe.

Kwamishinan INEC na jihar Osun Farfesa Abdulganiyu Raji, a wata hira da yayi da Channels Television ya ce saye da sayar da kuri’u laifi ne kuma INEC ba hukumar tsaro ba ce da za ta iya kama mutane kamar yadda Legit.NG ta rawaito.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tinubu ya sake samun gagarumin goyon baya daga tsohon gwamna

Kotu ta wanke wadanda suka gudanar da zanga-zangar 'Buhari Must Go'

A wani labari,Jihar Kogi - Wata kotun majistare da ke zamanta a jihar Kogi, a ranar Alhamis, ta saki wasu ‘yan rajin kare hakkin bil’adama guda biyu, da jihar yiwa hukunci saboda sun lika allunan zanga-zanga mai taken ‘Buhari must Go’ a watan Afrilun 2021. Rahoton Jaridar PUNCH

Alkalin kotun Mai shari’a Tanko Muhammed ya yi watsi da karar Amini Udoka da Emmanuel Larry mai lamba: CMCL/123m/2021 bayan an dage sauraron karar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa