Jita-jitar barin APC: Hadimin Farfesa Yemi Osinbajo ya fito, ya fadi gaskiyar lamari
- Akwai jita-jitar da ke yawo cewa Mataimakin shugaban kasa ya rubuta takarda zai bar jam’iyyar APC
- Fadar Shugaban kasa ta musanya jita-jitar, hakan ya nuna Farfesa Yemi Osinbajo bai sauya-sheka ba
- Laolu Akande wanda yake magana da yawun bakin Yemi Osinbajo, ya ce takardar ba ta gaskiya ba ce
Abuja - Mai girma Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya yi watsi da rade-radin da ake yi na cewa ya rubuta takardar fita daga jam’iyyar APC.
Daily Trust a rahoton da ta fitar a ranar Juma’a, 15 ga watan Yuli 2022, ta ce rahotannin da ke yawo na ficewar Yemi Osinbajo daga APC, karya ne.
Ana jita-jitar Farfesa Yemi Osinbajo ya aikawa Muhammadu Buhari takarda yana neman sauya-sheka, saboda APC ta ba Musulmi da Musulmi takara.
A wannan takarda mai lamba SH/VP/605/2./0 da ake yadawa, ana ikirarin Osinbajo ya bada dalilan da suka sa zai bar APC, har da matsin lamba daga gida.
Haka zalika takardar ta nuna mataimakin shugaban kasa ya gaji da cigaba da shiga harkar siyasa.
Martanin fadar shugaban kasa
Jaridar Daily Trust ta nemi jin ta bakin Mai magana da yawun bakin mataimakin shugaban Najeriyan, Laolu Akande a game da wannan takarda aka fitar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Laolu Akande ya tabbatar da cewa babu gaskiya a wannan batu, ya ce takardar ta karya ce.
Hadimin fadar shugaban kasar ya ce idan aka duba rubutun, za a fahimci ya sha bambam da na Farfesa Osinbajo, sannan cike takardar take da kura-kurai.
Wannan takarda daga ina? - Akande
“Ina ku mutane ku ke samo wannan abin? Wanene ya ba ku? Oho dai, domin a cire shakku, takardar bogi ce.”
“Mai girma mataimakin shugaban kasa (Farfesa Yemi Osinbajo) bai rubuta wani abu sam mai kama da wannan ba.”
Kamar yadda Punch ta fitar da rahoto dazu da safe, ta ce da manema labarai suka tuntubi Akande, ya sake irin wannan bayani, ya ce labarin karya ne ake yadawa.
Mai magana a madadin Farfesan yake cewa takardar cike ta ke da tarkace, kuma yadda aka tsara zancen bai yi kama da na mataimakin shugaban kasa ba.
Orubebe ya zama DG
Labari ya zo mana cewa tsohon jigon PDP, Godsday Elder Orubebe yana da farar kafa, shi ne zai jagoranci takarar Gwamnan APC a jihar Delta a zabe mai zuwa.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, kuma 'dan takarar Gwamna, Ovie Omo-Agege ya bada wannan sanarwa ta bakin Kakakin kamfe, Ima Niboro.
Asali: Legit.ng