2023: Kwamishinan Zulum ya maye gurbin Shettima a matsayin dan takarar APC a Borno ta tsakiya

2023: Kwamishinan Zulum ya maye gurbin Shettima a matsayin dan takarar APC a Borno ta tsakiya

  • Babban lauyan gwamnatin jihar Borno kuma kwamishinan shari’a, Barista Shehu Lawan, ya maye gurbin Kashim Shettima
  • Bola Ahmed Tinubu ya zabi Kashim Shettima a matsayin abokin takarar sa na zaben shugaban kasa a 2023
  • Barista Shehu Lawan ya yabawa Sanata Shettima akan kasancewarsa shugaba nagari ga ‘yan jam’iyyar APC a Borno

An zabi babban lauyan gwamnatin jihar Borno kuma kwamishinan shari’a, Barista Shehu Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai wakiltar Borno ta tsakiya a zaben 2023. Rahoton Daily Trust

Lawan ya maye gurbin Sanata Kashim Shettima, wanda aka tsayar a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar.

Shettima dai ya ajiye tikitin ne bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya zabe shi a matsayin abokin takararsa.

Kara karanta wannan

2023: Jerin sunayen yan takarar mataimakin shugaban kasa 10 da kwamitin APC ya gabatarwa Tinubu

Lawan
2023: Kwamishinan Zulum ya maye gurbin Shettima a matsayin dan takarar APC a Borno ta tsakiya FOTO Borno Express
Asali: UGC

A ranar alhamis din da ta gabata ne wakilai daga kananan hukumomi takwas na majalisar dattawa suka zabi Lawan a sakatariyar jam’iyyar dake Maiduguri.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kananan hukumomin su ne Maiduguri Metropolitan Council, Jere, Mafa, Bama, Dikwa, Konduga, Kalabalge da Ngala LGA’s da suka hada da mazabar Borno ta tsakiya inda suka zabe shi ba tare da hamayya ba.

Da yake jawabi bayan kammala zaben shugaban kwamitin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, Alhaji Uba Maigari Amadu, ya ce dan takarar jam’iyyar APC na jihar Borno ta tsakiya ya samu kuri’u 459 daga cikin kuri’u 480 da aka tantance.

Da yake mayar da martani bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, Lawan ya gode wa Gwamna Babagana Zulum bisa tsayin daka don tabbatar da hadin kan jam’iyyar.

Ya kuma yabawa Sanata Shettima bisa kasancewarsa shugaba nagari ga ‘yan jam’iyyar APC a Borno ya ce :

Kara karanta wannan

Ba za mu sake yiwa Tinubu kamfen ba saboda zabar Musulmi da ya yi, Kiristocin APC a arewa

"Idan aka zabe ni Senata, a matsayina na lauya, zan nuna kyakkyawan wakilci ga mutanen jihar Borno".

'Yan fashi: Matawalle ya bukaci da a tsawaita shekarun ritaya na jami'an tsaro zuwa 70

A wani labarin, Jihar Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Talata, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tsawaita wa’adin ritayar jami’an tsaro a Najeriya zuwa shekaru 70, inda ya kara da cewa ya kamata a tsawaita shekarun shiga aikin Short Service daga shekaru 30 zuwa 32 domin samun karin ma’aikata. Rahoton jaridar PUNCH

Sai kuma a ba wa maza da mata masu karfi jiki dake son shiga aikin jami’an tsaro damar yi wa kasar su hidima don tabbatar da tsaro a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa