Babban jigon PDP kuma shugaba a shiyyar arewa ta gabas ya fice daga jam'iyyar

Babban jigon PDP kuma shugaba a shiyyar arewa ta gabas ya fice daga jam'iyyar

  • Babban jigon PDP kuma ma'aji a reshen shiyyar arewa maso gabas, Abba Itas, ya yi murabus daga kasancewa mamban jam'iyya
  • Honorabul Abba ya bayyana cewa ya yi haka ne sakamakon rashin adalci da zaluntar da aka yi wa gwamna Wike na Ribas
  • Ya ce abubuwan da ke faruwa a babbar jam'iyyar hamayya ya nuna ba ta shirya kwace mulki ba a zaɓen 2023

Bauchi - Ma'aji na jam'iyyar PDP shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, Honorabul Galadima Abba Itas, ya yi murabus daga kasancewa mamban jam'iyya a jahar Bauchi.

Leadership ta ruwaito cewa ya sanar da matakinsa ne a wata takarda da ya aike wa shugaban PDP na gundumar Itas, ƙaramar hukumar Itas -Gadau mai ɗauke da kwanan watan 12 ga watan Yuli, 2022.

Kara karanta wannan

Rikicin APC ya kara ƙamari bayan zaɓo mataimakin Tinubu, wani babban ƙusa ya fice daga jam'iyyar

Abba Itas.
Babban jigon PDP kuma shugaba a shiyyar arewa ta gabas ya fice daga jam'iyyar Hoto: puncng.com
Asali: UGC

Ya ce ya yanke shawarin ne bayan faɗaɗa neman shawari da tawagar magoya bayansa, da kuma abokanansa na siyasa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Meyasa ya yanke ficewa daga PDP?

Honorabul Abba Itas ya ce ya ɗauki matakin ficewa daga PDP ne sakamakon rashin adalci da aka yi wa gwamnan Ribas, Nyesom Wike, yayin da kuma bayan zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng ta tattaro muku cewa gwamna Wike, wanda ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa na PDP, ya sha ƙasa ne a hannun tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar.

Abba Itas ya ce:

"Daɗin daɗawa aka biyo bayan haka da zaɓen gwamna Okowa na Delta a matsayin abokin takarar Atiku wanda hakan ya saɓa wa tsaruka da aƙidun siyasata don haka na yanke yin murabus."

Ya ƙara da bayanin cewa a matsayin mai faɗa a ji, "Rashin adalci da zaluntar," mambobin da suka kafa jam'iyya barazana ce ga haɗin kan jagorori da mambobi. makamantansa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Na sha baƙar wahala, na ƙagara mulkina ya kare na koma Daura, Buhari ya koka

A cewarsa, "Halin da ake ciki a jam'iyya ba zai ba da kwarin guiwar cewa ta shirya kwace mulki a babban zaɓen 2023 ba."

A wani labarin kun ji cewa Gwamnan Imo ya bugi ƙirji cewa kowane gwamnan APC zai tabbatar jam'iyyar ta yi nasara a jiharsa a zaɓen 2023

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya yi ikirarin cewa kowane gwamna daga cikin gwamnonin cigaba na APC zai tabbatar jam'iyya ta yi nasara a jiharsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Ya ce kasancewar gwamnonin sun yi abin da ya dace, al'ummar jihohin su zasu sake kaɗa wa APC kuri'un su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262