Shugaban ƙasa a 2023: Gwamnoni 22 zasu tabbatar APC ta yi nasara a jihohin su, Uzodinma

Shugaban ƙasa a 2023: Gwamnoni 22 zasu tabbatar APC ta yi nasara a jihohin su, Uzodinma

  • Gwamnan Imo ya ce kowane gwamna daga cikin gwamnonin APC 22 zai kawo wa APC jiharsa a zaɓen shugaban ƙasa 2023
  • Ya ce kasancewar gwamnonin sun yi abin da ya dace, al'ummar jihohin su zasu sake kaɗa wa APC kuri'un su
  • Gwamnonin, yayin ziyarar barka da Sallah ga Buhari a Daura, sun ce zaben Shetima a mataimakin Tinubu zaɓi ne na kowa

Daura, jihar Katsina - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya yi ikirarin cewa kowane gwamna daga cikin gwamnonin cigaba na APC zai tabbatar jam'iyya ta yi nasara a jiharsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Uzodimma ya yi wannan furucin ne a Daura, jihar Katsina lokacin da suka je ziyarar barka da Sallah ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Gwamnonin APC a Daura tare da Buhari.
Shugaban ƙasa a 2023: Gwamnoni 22 zasu tabbatar APC ta yi nasara a jihohin su, Uzodinma Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

"Gwamnoni 22 zasu kawo baki ɗaya jihohin su saboda sun yi abin da ya dace," a lafazin gwamna Uzodinma. "Saura jihohi nawa suka rage kenan?"

Kara karanta wannan

Gwamnoni 9 sun dira gidan shugaban kasa a Daura, sun sa labule da Buhari

Uzodimma ya bayyana cewa matakin Bola Ahmed Tinubu na zaɓo Sanata Ƙassim Shettima a matsayin abokin takararsa a zaɓen shugaban ƙasa, "abu ne da kowa ya amince da shi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya je Daura ne tare da takwarorinsa na jam'iyyar APC Takwas da suka haɗa da, Aminu Masari na Katsina, Abdullahi Ganduje na Kano, Masir El-Rufai na Kaduna da Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Sauran gwamnonin sune: Abubakar Bello na Neja, Kyode Fayemi na jihar Ekiti, Simom Lalong na jihar Filato da gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.

Ko ya gwamnonin suka ɗauki zaɓin Tinubu?

Gwamnonin sun bayyana zakulo tsohon gwamnan Bornon a matsayin wanda ya fi kyau da kuma dace wa.

Da yaƙe jawabin bayan ganawar sirri da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu, ya ce shugabancin Tinubu-Shettima zai haskaka nasarorin Buhari na shekaru Bakwai.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Ganduje ya faɗi wanda Bola Tinubu ya amince zai zaɓa a matsayin mataimaki na gaske

Gwamna Bagudu ya ƙara da cewa ƙungiyar gwamnoni sun matsa kaimi suna aiki ba dare ba rana domin ganin jam'iyyar ta lashe zaɓen gwamnan jihar Osun da ke tafe.

A wani labarin kuma kun ji cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya shiga ganawar sirri da gwamnoni 9da suka kai masa ziyara har Daura

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da gwamnonin jam'iyyar APC Tara sun shiga ganawa a mahaifar shugaban, Daura a jihar Katsina.

Sun shiga gana wa da shugaban ƙasan ne bisa jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin cigaba na APC kuma gwamnan Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262