Babban Lauyan Najeriya ya raba gardama game da takarar Musulmi da Musulmi a APC

Babban Lauyan Najeriya ya raba gardama game da takarar Musulmi da Musulmi a APC

  • Babatunde Ogala ya yi bayanin abin da dokar kasa da tsarin mulki suka ce a game da takara
  • Babban Lauyan ya ce babu ruwan kundin tsarin mulki da addini wajen tsaida takara a Najeriya
  • Ogala ya kare Tinubu, yana ganin kamata ya yi a yabawa ‘Dan takaran na APC, ba a kushe shi ba

Abuja - A karon farko a cikin shekaru kusan 30, babbar jam’iyyar siyasa a Najeriya ta zabi ‘yan takararta na zaben shugaban kasa duk su zama Musulmai.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa Babatunde Ogala wanda Lauya ne wanda ya kai matsayin SAN a Najeriya, ya tsoma baki a kan takarar APC a zaben 2023.

Babatunde Ogala SAN yake cewa Bola Ahmed Tinubu bai saba wata doka saboda ya zabi Musulmi ya zama abokin takararsa, duk da shi yana Musulmin ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari ya fito yana adawa da takarar Musulmi-Musulmi

Da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV, Ogala ya kare Mai gidansa a game da daukar Musulmi da ya yi, ya jawo tikitin Musulmi-Musulmi.

Ogala shi ne shugaban sashen shari’a na kwamitin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu a 2023, ya kuma yi karin-haske a kan abin da tsarin mulki ya ce.

“Tinubu ya yi wani abin da ya sabawa damar da doka ta ba shi wajen daukar abokin takara? Dole mu komawa sashe na 14 da 15 na dokar kasa.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bola Tinubu wajen kamfe Hoto: @officialasiwajubat
APC da Bola Tinubu wajen kamfe Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook
“Dokar ta yi maganar adalci da gaskiya wajen rabon dukiyar kasa, amma ba ta kawo batun addini ba.
“Dokar ta yi bayanin bambance-bambance da wakilcin al’umma. Tsarin mulki bai yi batun addini ba, saboda haka ba zai yiwu ace an ware wasu ba.”

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi karin-haske a kan ‘goyon bayan’ APC da Bola Tinubu a zaben 2023

- Babatunde Ogala SAN

Rahoton yake cewa Ogala ya nemi a yabawa ‘dan takaran shugaban kasar na APC ne saboda ya dauko mutum daga yankin da ba su da rinjaye a siyasar kasar.

“Mu na da manyan kabilu uku a Najeriya – Hausa/Fulani, Yarbawa da Ibo. Mu na lura da marasa rinjaye, irinsu Kashim Shetimma – Kanuri daga Borno?

Babban lauyan yake cewa kowace jam’iyya ta fito lashe zaben 2023 ne, wannan ya sa dole ‘dan takara ya yi duk abin da zai taimaka masa wajen yin nasara.

APC ta yi kokarin ba ‘Dan Kudu tikiti a zaben 2023, abin da PDP ta gagara yi, inji Ogala wanda yake sa ran cewa Sanata Kashim zai kai jam’iyyar ga cin zabe.

Gwamnonin APC sun hadu a Daura

Kun samu labari Gwamnoni sun nuna rashin jin dadin yadda Bola Tinubu ya dauko abokin takarara. Hakan ta sa Gwamnonin su ka yi zama da Shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Idan na rasa kujerar Buhari, kowa ma ya rasa, amma Tinubu ya samu

Daga baya Shugaba Muhammadu Buhari ya lallashi Gwamnonin jam’iyyarsa, a karshe suka amince Kashim Shettima ya rike tutar jam’iyyar APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng