Yadda Buhari ya shawo kan Gwamnonin APC a kan zaben Shettima da Tinubu ya yi

Yadda Buhari ya shawo kan Gwamnonin APC a kan zaben Shettima da Tinubu ya yi

  • Gwamnonin APC sun yi zama da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan batun zaben 2023
  • Wadannan Gwamnoni sun nuna rashin jin dadin yadda Bola Tinubu ya dauko abokin takararsa
  • Daga baya Shugaban kasa ya lallashi Gwamnonin, hakan ta sa suka amince da Kashim Shettima

Katsina - A ranar Litinin, 11 ga watan Yuli 2022, gwamnonin jihohin APC suka yi wani zama na musamman da Mai girma Muhammadu Buhari a Daura.

Rahoton da Punch ta fitar ya nuna cewa gwamnonin sun nuna rashin jin dadinsu a game da yadda Bola Tinubu ya tsaida abokin takararsa na zabe mai zuwa.

Gwamnonin da suka samu zuwa wannan taro sun yarda Tinubu yana da damar zabar wanda yake so a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

2023: Na sanyawa Tinubu da Shettima albarka, in ji Ali Modu Sheriff

Sai dai gwamnonin sun ce ba su karkare magana da ‘dan takaran shugaban kasar na APC ba, sai suka ji ya sanar da Duniya cewa ya dauki Kashim Shettima.

Ba haka aka so ba

Majiyar ta shaidawa jaridar cewa Gwamnonin na APC sun yi sha’awar a ba Gwamna Atiku Bagudu ko Nasir El-Rufai tikitin mataimakin shugaban kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dalilinsu shi ne wadannan gwamnoni na Jihohin Kebbi da Kaduna sun fito daga inda ake da yawan kuri’u. Yankin Arewa maso yamma sun fi ko ina jama’a.

Gwamnonin APC
Wasu Gwamnonin APC a Daura Hoto: BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Rahoton yace gwamnonin jam’iyya mai mulki ba su ji dadin samun labari Tinubu ya zabi tsohon Gwamnan na jihar Borno a matsayin abokin neman takarara ba.

Buhari ya shigo maganar

Hadimin wani daga cikin Gwamnonin ya fadawa Punch cewa shugaba Muhammadu Buhari ya lallashi Gwamnoni a taron da suka amince da Kashim Shettima.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi karin-haske a kan ‘goyon bayan’ APC da Bola Tinubu a zaben 2023

Buhari ya nuna masu cewa Sanata Kashim Shettima yana yi wa jam’iyyar mai mulki biyayya.

A talabijin ne Gwamnonin suka samu wannan labari kamar sauran mutanen kasar, wanda hakan ya yi masu ciwo kafin shugaban Najeriya ya sa baki da aka zauna.

Buhari ya kebe da Gwamnoni

Legit.ng Hausa ta kawo rahoto Gwamnoni goma ne aka yi wannan zama da su a garin Daura, jihar Katsina. Akwai Gwamnonin APC fiye da 10 da ba a gani ba.

Da suka fito su na magana, kungiyar gwamnonin APC ta bakin shugabansu, Gwamna Abubakar Bagudu, sun tabbatar da sun yi mamakin samun labarin Shettima.

Sai dai duk da haka, shugaban kungiyar PGF ya bayyana cewa Shettima cancanci ya zama abokin takara, ya kuma ce zai karfafi tafiyar Bola Tinubu a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng