Tikitin Tinubu/Shettima: Adamu Garba ya sake komawa jam’iyyar APC
- Gabannin zaben shugaban kasa na 2023, Adamu Garba ya sake ficewa daga jam'iyyar Young Progressives Party (YPP) zuwa APC
- Garba ya ce zai cutar da kasarsa Najeriya idan har bai goyi bayan tikitin Tinubu da Shettima ba a zabe mai zuwa
- Hakan na zuwa ne bayan dan siyasar ya bayyana cewa matasa basu da makoma a karkashin jam'iyyun APC da PDP
Shahararren dan siyasa Adamu Garba ya sake komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan ya sauya sheka zuwa Young Progressives Party (YPP).
Garba ya bar jam’iyya mai mulki don yin takarar tikitin shugaban kasa a jam’iyyar YPP, amma sai ya sha kaye a hannun Malik Ado-Ibrahim.
Da ya mallaki fom din takarar shugaban kasa na YPP a watan Mayu, Garba ya ce matasa basu da makoma a jam’iyyar APC da Peoples Democratic Party (PDP).
Ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Ni dan PDP mai karfi ne a 1999, a 2003 mun koma ANPP sannan a 2007 muka koma PDP inda muka tsaya har 2014 lokacin da aka kafa APC sannan muka koma cikinta.”
Amma a wata wallafa da ya yi a shafin Twitter a ranar Talata, dan siyasar ya ce ya koma jam’iyyar mai mulki a kasar, kuma cewa zai zama cutarwa ga kasar idan ya ki marawa Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC da mataimakinsa, Kashim Shettima baya.
Ya rubuta a shafin nasa:
“Eh, na dawo APC gaba daya. Zan iya cutar da kasata Najeriya idan ban goyi bayan wannan hadi na manyan masu dabaru a tikiti daya ba.
“BAT/Hashim ne ya kamata su karbe dukkanin mazabu a Najeriya a 2023. Na sake sauya sheka!”
2023: Na sanyawa Tinubu da Shettima albarka, in ji Ali Modu Sheriff
A gefe guda, tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, ya ce ya sanyawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima albarka.
Sheriff ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murna dauke da sa hannun Cairo Ojougboh, Darakta Janar na kungiyar kamfen din Ali Modu Sheriff.
Martaninsa na zuwa ne kimanin awa 24 bayan Tinubu ya sanar da Mista Shettima, tsohon gwamna kuma sanata mai ci a matsayin abokin takararsa, Premium Times ta rahoto.
Asali: Legit.ng