Bukola Saraki ya tanka shirin Gwamnonin APC na dauke Wike daga PDP

Bukola Saraki ya tanka shirin Gwamnonin APC na dauke Wike daga PDP

  • Bukola Saraki ya jaddada cewa Gwamna Nyesom Wike yana da muhimmanci sosai a jam’iyyar PDP
  • Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce zaman Gwamnonin APC da Wike ba zai haifar da komai ba
  • Dr. Saraki ya nuna PDP ba za ta bari Wike ya sauya sheka ba saboda muhimmancin zaben 2023

Kwara - Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya maida martani bayan ganin alamun jam’iyyar APC ta na zawarcin Nyesom Wike.

Dr. Bukola Saraki ya yi magana ne a ranar Asabar, 9 ga watan Yuli 2022, biyo bayan ziyarar da gwamnonin APC suka kai wa Gwamnan Ribas, Nyesom Wike.

The Cable ta rahoto cewa babban jigon na jam’iyyar PDP ya ce za su zauna domin dinke duk wata baraka domin ganin an kifar da gwamnatin APC a 2023.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ce Najeriya ta cikin matsanancin yanayi

Saraki ya bayyana cewa Gwamna Wike yana cikin ‘ya ‘yan da jam’iyyar adawa ta PDP ta ke ji da su.

Bukola Saraki a kan Nyesom Wike

“Gwamna Wike yana cikin masu muhimmanci a ‘ya ‘yan jam’iyyarmu, ina sa ran ba da dadewa ba, za mu zauna domin shawo kan komai.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Shakka babu, ba laifi ba ne ganin yadda ya tsinci kan shi, amma akwai hanyoyin da za a bi domin magance matsaloli irin wannan.”
Gwamnonin APC a Fatakwal
Fayose, Wike da Gwamnonin APC Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC
“Abin farin cikin shi ne, mu na magana da juna. Mu na neman fin karfin lamarin, za mu hada-kai, mu yi kokarin cin zabe mai zuwa.”
“Ina tabbatar maku da jam’iyyar PDP za ta magance matsalolin cikin gidanta.”

Bukola Saraki

A rahoton da ya fito daga Tribune, tsohon gwamnan na jihar Kwara ya ce APC ba za ta iya ribata da Wike ba, ya kuma yi magana a kan yajin-aikin ASUU.

Kara karanta wannan

Okupe: Abin da ya sa tun tuni Peter Obi ya yi watsi da maganar dunkulewa da Kwankwaso

Abin nema ya samu

“Gwamnonin APC sun san irin wannan tsagewar suke neman domin samun hanyar wucewa. Abin fain cikin shi ne ba za mu ba su shi (Wike) ba.”
“Zabe mai zuwa yana da matukar muhimmanci. Makomar miliyoyin mutanen Najeriya ta fi karfin wata jam’iyya ko kuma wani mutum daya.”
“Ina farin ciki da duk masu ruwa da tsakinmu da shi kan shi Wike ya yarda da hakan.”

Bukola Saraki

Kuran da aka yi ga Tinubu

Kun ji yadda Kungiyar CNYY da APC Media and Mobilisation for BAT’23 su ka ba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shawarar wanda ya dace ya dauka a 2023.

Kungiyar Yarbawan Arewa ta bada sunan wani Fasto a Gwamnatin nan yayin da magoya bayan Tinubu su ka ce, Nasir El-Rufai ya dace da abokin takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng