Kungiyar Atiku Ta Nesanta Kanta Daga Rikicin PDP a jihar Ekiti
- Kungiyar Atiku Mobilisers’(TAM) ta barrantar da Alhaji Atiku Abubakar daga rikicin cikin gida da jihar Ekiti ke fuskanta
- Wasu na gani rikicin jam'iyyar PDP na jihar Ekiti na da alaka da matsalar dake tsakanin Nyesom Wike da Atiku Abubakar
- Sashen Fayose sun zabi Alaba Agboola a matsayin shugaban jam'iyyar sai kuma yan adawar sa sun zabi Hon Bisi Kolawole
Jihar Ekiti - Wata kungiya dake taya tsohon mataimakin shugabankasa Alhaji Atiku Abubakar yakin neman zaben a jam’iyyar PDP, a zaben mai zuwa, ta nesanta kanta da rikicin bangaranci da ya dabaibaye jam’iyyar a jihar Ekiti kamar yadda jaridar THIS DAY ta rawaito.
Kungiyar mai taken: ‘Atiku Mobilisers’ (TAM) ta yi nadamar yadda jam’iyyar PDP ta jihar ta kasu gida biyu, inda ta bukaci uwar jam’iyya karkashin jagorancin Dr. Iyorchia da su sa baki a cikin lamarin dan kawo karshen matsalar kamar yadda jaridar The SUN ta rawaito.
A ranar Litinin din da ta gabata ne kwamitin ayyuka NWC da ke biyayya ga tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ta zabi Alaba Agboola, makusancin Sanata Biodun Olujimi, a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon Shugaban Jam’iyyar Jihar, Hon Bisi Kolawole.
A wani taro da kwamitin NWC dake adawa fayose suka gudanar a Ado Ekiti, tsohon shugaban karamar hukumar Ado Ekiti, Hon. Deji Ogunsakin, suka zaba a matsayin shugaban jam’iyya na jiha.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wasu suna fassara Ricikin cikin gida da ta baibaye jam’iyyar PDPn jihar Ekiti da cewa matsalar da ke tsakanin Atiku da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike wanda fitaccen aminin Fayose ne ya janyo haka.
Sai dai sanarwar da ta fitar bayan taron ta da ta gudanar a Ado Ekiti a jiya tare da sanya hannun ‘yan kungiyar 22, ta ce babu hanun kungiyar da shugabanta da rikicin cikin gida da jam’iyyar PDP na jihar Ekiti ke fuskanta.
Harin Kuje: ‘Allah ne kadai ya cece mu’ – Abba Kyari ya bada labarin abun da yafaru
Bayan harin da yan bidigan kungiyar ISWAP suka kaiwa gidan yarin Kuje a daren ranar Talata ya lafa.
Dakataccen tsohon Mataimakin kwamshinan yansanda DCP Abba Kyari wanda fursuna ne a gidan yari ya ba da labarin abin da ya auku a ranar harin, Rahton jaridar VANGUARD.
Asali: Legit.ng