‘Dan takaran Shugaban kasa ya sharara karya game da wutar lantarkin Najeriya
- Tolu Ogunlesi ya maidawa Peter Obi martani game da ikirarin da ya yi kan yarjejeniyar Siemens
- A baya an ji Obi yana cewa kamfanin Siemens sun fada masa aikin wutan Najeriya bai je ko ina ba
- Hadimin shugaba Muhammadu Buhari ya zargi ‘dan takaran jam’iyyar LP da yi wa mutane karya
Abuja - Hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi, ya zargi Peter Obi da yin karya a bayanin da ya yi a kan yarjejeniyar gwamnatin tarayya da Siemens.
A wani bayani da ya yi a Twitter, Tolu Ogunlesi ya ce babu yadda za ayi mutum ya yi ikirarin babu abin da kamfanin Siemens ya yi kan harkar wuta.
Mai ba shugaba Muhammadu Buhari shawara yake cewa kamfanin ya yi abubuwa da yawa domin inganta lantarki, akasin ikirarin na Mista Peter Obi.
A wani bidiyo da yake yawo a yanar gizo, an ji Obi yana yi wa mutane bayani cewa aikin samar da wutan bai yi nisan komai ba, in ban da surutu kurum.
Da yake karin-haske a shafinsa, Ogunlesi ya ce maganar gaskiya ‘dan takara na LP ya yi karya, kuma bai kamata a bar maganar da ya yi ta tafi a haka ba.
Hadimin shugaban kasar yake cewa za a fara gwajin kayan aikin da aka tanada a wannan watan. Nairametrics ta fitar da wannan rahoto a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganar Tolu Ogunlesi
"Akwai bidiyon Peter Obi yana cewa kamfanin Siemens sun fada masa Najeriya na ta yin zama da su, amma babu wani cigaba da aka iya samu.
Tare da girmamawa, wannan ma wata karya ce da bai kamata a bari ba a maida martani ba.
Bayan fara aikin PPInigeria, FGNPowerCo sun yi nisa, kuma har an kammala. An nada wanda zai rika bada shawara da aka sa hannu a yarjejeniya a 2021.
Wani ya yi da’awar an fama masa wannan, musamman daga bakin kamfanin da ke aiki – tsagwaron karya ce, kuma zai yi saukin gano gaskiya.
Ya kamata a rika bibiyar gidan labaran PPInigeria news – domin ana kawo duka labaran nan."
Shirin zaben 2023
Dazu mu ka ji labari cewa ‘Yan Keke Marwa Coalition sun roki ‘Dan takaran APC ya dauko tsohon Gwamnan Soja na Legas ya zama Mataimakinsa.
Kungiyar ta ce Janar Buba Marwa mai ritaya wanda shi ne shugaban NDLEA ya cancanci ya zama ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa a APC.
Asali: Legit.ng