2023: Jam'iyyar APC ta fara kokarin hana guguwar sauya sheka ta yi awon gaba da Mambobinta a Kebbi

2023: Jam'iyyar APC ta fara kokarin hana guguwar sauya sheka ta yi awon gaba da Mambobinta a Kebbi

  • Alamu sun nuna uwar jam'iyyar APC ta tsoma baki domin shawo kan rikicin da ke kwashe mata 'ya'ya a jihar Kebbi
  • Jam'iyya mai mulki ta kira taron masu ruwa da tsaki da mambobin da ran su ya ɓaci domin tattauna wa da kuma yin sulhu
  • Mataimakin shugaban APC na shiyyar arewa maso yamma ya ce duk da abinda ke faruwa hangen nasara kawai yake wa jam'iyyarsa a 2023

Kebbi - Jam'iyyar APC ta soma shirin daƙile yunkurin guguwar sauya sheƙa na ɗibar jiga-jigai da mambobinta zuwa babbar jam'iyyar hamayya PDP a jihar Kebbi.

Daily Trust ta ruwiato cewa jam'iyyar ta kira taron masu ruwa da tsaki domin sasanta wa da mambobi waɗan da suka fusata da nufin daƙile yunkirinsu na sauya sheƙa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban APC na shiyyar wata jiha da dubba mambobin sun koma PDP

Ba da jimawa ba jam'iyyar APC ta yi rashin wasu manyan jiga-jiganta zuwa tsagin hamayya bisa dalilai daban-daban duk a jihar ta Kebbi.

Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, na jam'iyyar APC.
2023: Jam'iyyar APC ta fara kokarin hana guguwar sauya sheka ta yi awon gaba da Mambobinta a Kebbi Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Daga cikin waɗan da APC ta rasa sun haɗa da Sanata Adamu Aleiru, Dakta Yahaya Abdullahi, da kuma mamba a majalisar wakilan tarayya, Barista Mohammed Bello Yakubu, Mohammed Umar Jega da Abdullahi Zumbo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka nan mambobin majalisar dokokin jihar da suka haɗa da, Habibu Labbo, Ismaila Bui da kuma Mohammed Buhari Aliero, sun bi sahu wajen ficewa daga APC, jaridar Guardian ta ruwaito.

Da yake jawabi a wurin taron sulhun, mataimakin shugaban jam'iyya na shiyyar arewata ta yamma, Salisu Lukman, ya ce taron ya maida hankali wajen kokarin shawo kan saɓanin da aka samu tsakanin jiga-jigan jam'iyya a Kebbi.

Lukman ya ce:

Kara karanta wannan

Saba alkawari: Ta karewa APC a Sokoto, 'yan kasuwa sun yi watsi da ita sun koma PDP

"Duk da guguwar sauya shekar da ta turnuƙe jam'iyya ta ɗibi mambobi, ina ji a raina APC ce jam'iyyar da zata samu nasara a 2023. Har yanzun ina ganin haɗin kan mambobi kuma hakan alama ce ta nasara."

Meyasa suka kira taron?

Mataimakin shugaban ya ƙara da cewa jam'iyya mai mulki ta na buƙatar kowane mambanta ya ci nasara a babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Bugu da ƙari, Lukman ya yi bayanin cewa sun kira wannan taron ne domin jin ta bakin fusatattun mambobi domin duba yuwuwar warware matsalar a matakin ƙasa.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun kai wa tawagar motocin shugaba Buhari hari a jihar Katsina

'Yan bindiga sun far wa tawagar motocin shugaban ƙasa Buhari a kan hanyar su ta zuwa Daura a shirye-shiryen zuwa Babbar Sallah.

Malam Garba Shehu, ya ce tawagar ta ƙunshi, hadimai, ma'aikata da yan jaridar gidan gwamnati amma Buhati baya ciki.

Kara karanta wannan

Mayaƙan ISWAP da suka yi yunkurin kai kazamin hari Monguno da motocin yaƙi sun kwashi kashin su a hannun Sojoji

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262