2023: Idan Har Ka Ajiye Okowa, Ba Zaka Samu Kuri'an Igbo Ba, Matasan Ohanaeze Sun Gargadi Atiku Da PDP
- Kungiyar matasan Igbo ta OYC ta gargadi jam'iyyar PDP da dan takarar shugaban kasarta Atiku Abubakar kan canja Okowa a matsayin mataimakinsa
- Matasan na Igbo sun ce muddin Atiku ya sauya Okowa da Wike, ba za su jefa wa jam'iyyar ta PDP kuri'a ba
- Shugaban OYC, Mazi Okwu Nnabuike da Sakatarenta, Obinna Achionye ne suka fitar da sanarwar suna mai cewa Igbo ba za su yadda a ware su ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Matasan Igbo karkashin kungiyar Ohanaeze Ndigbo Youth Council Worldwide, OYC, ta gargadi dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar kan duk wani shiri na ajiye Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa.
A cikin da shugabannin kungiyar suka raba wa yan jarida a ranar Talata, ta ce idan Atiku ya ajiye Okowa, duk abin ya faru, shi ya janyo, rahoton Vanguard.
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban OYC na kasa, Mazi Okwu Nnabuike da Sakatarenta, Obinna Achionye ta ce duk wani yunkuri na canja Okowa ba zai haifar da alheri ba.
Kungiyar ta Igbo ta ce Kudu maso Gabas ba za ta yi bari a ware ta baki daya ba, duba da cewa ta rasa tikitin shugaban kasa a PDP da APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Babu bukatar maimaita cewa munyi tsamanin APC da PDP su bawa kudu tikitin takarar shugaban kasa amma hakan bai faru ba.
"Abin da kawai ya share mana hawaye shine zaben Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin Alhaji Atiku Abubakar, duba da cewa Okowa asalin Igbo ne.
"Ta yaya wani zai farka ya yi tunanin maye gurbin OKowa da Wike? Duk da mun san Atiku na da ikon zaben mataimakinsa, muma muna da ikon jefa wa wanda muke so kuri'a."
Kungiyar ta OYC ta cigaba da cewa PDP ba za ta samu wani kuri'a daga Igbo ba idan ta tsayar da Wike saboda ya taba cewa ba shi ba su. Sun ce suma sun raba jiha da shi don haka idan PDP ta zabe shi za a juya mata baya yayin zaben shugaban kasa.
Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa
A wani rahoton, Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers, wanda ya sha kaye hannun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya saki magana mai daure kai a dandalin sada zumunta.
A wani wallafa a Facebook a ranar Alhamis, Joe Igbokwe, jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya yi ikirarin cewa Wike ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu a Faransa.
Asali: Legit.ng