Gaskiya ta fito: Hotuna sun nuna lokacin da Tinubu ke matashi, ya halarci jami'a a Turai

Gaskiya ta fito: Hotuna sun nuna lokacin da Tinubu ke matashi, ya halarci jami'a a Turai

  • Wani hoto na zamanin da ya fito daga taskar ajiyan jami’ar Chicago kuma tuni ya karade shafukan soshiyal midiya
  • Kundin hotunan na dauke da fuskokin daliban da aka yaye a wata shekara da ba a bayyana ba da kuma sunayensu
  • Sai dai kuma, wani abu da ya fi jan hankali shine bayyanar fuskar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a cikin hotunan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Takaddamar da ke kewaye da batan takardar karatun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress mai mulki, Bola Ahmed Tinubu, ta zo karshe.

A safiyar yau Litinin, 4 ga watan Yuli, ne wata kundin hotuna na jami’ar Chicago ta bayyana a shafukan sosahiyal midiya.

Hotunan dalibai
Gaskiya ta fito: Hotuna sun nuna lokacin da Tinubu ke matashi, ya halarci jami'a a Turai Hoto: Joe Igbokwe
Asali: Facebook

Kundin hotunan wanda ya kasance a baki da fari yana dauke da fuskokin dalibai da aka yaye ciki harda Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

2023: Cikakkun sunayen yan takara da ke fama da batan takardun karatu a fadin jam’iyyun siyasa

Idan za ku tuna, Legit.ng ta rahoto a baya cewa jami’ar Chicago ta tabbatar da cewar Tinubu ya halarci jami’ar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Biyo bayan zarge-zarge da ake ta yi, Farooq Kperogi, wani lakcara dan Najeriya mazaunin Turai, ya ce ya je ga wani abokin aikinsa a jami’ar Chicago don ya taimaka masa wajen tabbatar da ko Tinubu ya kammala karatu a makarantar.

Takwaran nasa, bayan ya tabbatar daga ofishin magatakardar, sai ya wallafa martanin jami’ar.

"Saboda shakku game da takardar karatun Tinubu, na sake tuntubar wata abokiyar aikina a Jami'ar Jihar Chicago don taimaka mini wajen tabbatar da ko Tinubu ya kammala karatunsa a makarantar.
“Ta fada mani cewa ya kammala amma za ta je ta tambayi ofishin magatakarda. Ta tura mani wannan,” ya rubuta a shafin Twitter.

2023: Cikakkun sunayen yan takara da ke fama da batan takardun karatu a fadin jam’iyyun siyasa

Kara karanta wannan

Tinubu ya katange ni daga yakin neman zabensa saboda na janye wa Osinbao - Dr Felix

A gefe guda, gabannin zaben shugaban kasa na 2023, sabbin abubuwa na ta kunno kai tsakanin yan takarar shugaban kasa da abokan takararsu.

Kafin yanzu, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a shirinta na tantance yan takara don shiga zaben, ta bukaci masu neman takarar na jam’iyyun siyasa daban-daban su gabatar da wasu takardu don tantancewa.

Sai dai kuma, a inda yawancin yan takara ke samun babban matsala shine wajen gabatar da takardar shaidar karatunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng