2023: Dan takarar gwamna a Kaduna ya hada kai da 'yan Shi'a don nemawa Peter Obi kuri'u
- Dan takarar jam'iyyar Labour na gwamna a jihar Kaduna ya bayyana yadda yake neman goyon bayan wadanda aka cuta
- Ya bayyana cewa, jam'iyyarsa tana aiki ne don ganin hada kan kowa kuma a ba da gudunmawa na gari wajen gyara kasa
- A wannan karo, ya ce ya gana da shugabannin kungiyar Shi'a a Kaduna domin nemawa jam'iyyar LP da Peter Obi kuri'u
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Kaduna - Dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour a jihar Kaduna, Mista Shunom Adinga, ya ce ya kulla alaka da kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) domin neman goyon bayansu ga ‘yan takarar jam’iyyar ciki har da Peter Obi, a 2023.
Ya ce jam’iyyar LP za ta yi kokarin ganin an kawo dukkanin kungiyoyin da ke fama da rikici a kasar nan zuwa dandalin zaman siyasa domin su ba da gudummawarsu wajen kawo ci gaban kasar, Daily Trust ta ruwaito.
Dan takarar gwamnan na LP wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta jihar Kaduna, ya kuma bukaci kungiyar IMN da sauran ‘yan Najeriya da su marawa takarar sa da ta Obi baya.
A kalamansa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Muna iya bakin kokarinmu mu hada kan al’ummar da ke cikin rikici kamar kungiyar Shi’a, wato ta El-Zazaky. Mun nemi goyon bayansu. Mun samu cikakkiyar fahimta tare da su don hada kai da gwamnati mai jiran gado ta Peter Obi.”
Ya kuma yi ikirarin cewa, babu wata jam’iyya da ta shahara a kasar nan kamar jam’iyyar Labour saboda Najeriya ta fi yawan ma’aikata fiye da yawan ‘yan siyasa, inda ya ce babban bangaren kwarewarsa shi ne harkar dauakr ma'aikata.
Ya bayyana jam'iyyar Labour a matsayin babbar jam'iyyar da ke da yawan jama'a a kasar.
Akan batun malaman da ke rasa ayyukansu a Kaduna, ya ce gwamnatin da ba za ta iya hada kai da ma’aikatanta ba tare da ba su tsarin gudanar da aiki nagari lallai ta rasa tunani mai kyau, rahoton Tribune Online.
Babu yankin da zai iya samar da shugaban kasa shi kadai, inji kungiyar Afenifere
A wani labarn, kungiyar Afenifere ta bukaci ‘yan siyasa daga yankin Kudu maso Yamma da su hada kai da sauran shiyyoyi biyar na kasar domin tabbatar da aniyar tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, na zama shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa ya yiwu. rahoton PUNCH.
Sakataren Yada Labarai na Afenifere, Michael Ogungbemi, ya yabawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kungiyar gwamnonin APC, yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC da suka janye wa Tinubu da ‘ya’yan jam’iyyar da suka yi ruwa da tsaki dan ganin ya samu damar tsayawa takarar, inda suka ce:
“Yanzu lokaci ya yi da yankin Kudu maso Yamma za su nuna hadin kan da ba a taba gani ba don nuna wa ‘ya’yan jam’iyyar APC godewa.
Asali: Legit.ng