2023: Babu ɗan takarar kudu maso gabas da ya kama kafar Kwankwaso, Galadima

2023: Babu ɗan takarar kudu maso gabas da ya kama kafar Kwankwaso, Galadima

  • Buba Galadima, tsohon makusancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce lokaci ya yi da Kwankwaso zai karɓi Najeriya
  • Galadima ya yi ikirarin cewa babu wani ɗan takara daga kudu maso gabas da ya yi imani da haɗewar sabuwar Najeriya kamar Kwankwaso
  • Ya ce tun shekara 30 nan baya suka fara aikin ganin an gina sabuwar Najeriya kuma Kwankwaso ne zai iya

Abuja - Tsohon abokin fafutukar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ya ce babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa daga kudu maso gabas da ya kama kafar Rabiu Kwankwaso wajen ra'ayin gina sabuwar Najeriya.

Galadima, wanda ya yi wannan ikirarin ranar Litinin yayin zantawa da Arise TV, ya ce burin Kwankwaso na gina sabuwar Najeriya ya samo asali ne shekara 30 da suka gabata.

Buba Galadima.
2023: Babu ɗan takarar kudu maso gabas da ya kama kafar Kwankwaso, Galadima Hoto: vanguardngr.com

Jaridar Vanguard ta rahoto, Buba Galadima, mamba a jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, na cewa:

Kara karanta wannan

Kungiyar Afenifere tayi kira ga jiga-jigan yan siyasan Yarabawa su marawa Tinubu baya

"Babu wani ɗan takara daga yankin kudu maso gabas da ya yi imani da sabuwar Najeriya kamar yadda muka yi, muna buƙatar wani mutum wanda ya yarda da dunƙulewar Najeriya, ba rabe-raben Najeriya ba."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Tun shekara 30 da suka gabata muke aikin ganin mun aiwatar da wannan kudirin."

Meyasa Kwankwaso ba zai koma mataimakin Obi ba?

Yayin da aka tamabaye shi ko mai zai hana Kwankwaso ya hakura ya koma mataimakin Peter Obi, Galadima ya ƙara da cewa:

"Lissafin ya zarce Peter Obi, Sanata Kwankwaso ne kaɗai zai iya cika kudirin sabuwar Najeriya. Wannan shi ne lokacin da ya dace Kwankwaso ya karbi ragamar shugabancin ƙasar nan"

Idan baku manta ba, Kwankwaso da kansa ya faɗi dalilin da ya sa ba zai koma mataimakin Obi (ɗan takarar shugaban ƙasa na LP) ba a dai-dai lokacin da kiraye-kiraye suka yawaita kan yan siyasan biyu su haɗa kai su kawo karshen APC, PDP.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya sun gaji da APC, Kwankwaso ya ce ya hango karshen APC

Haka nan kuma tsohon gwamnan Kano ya nuna sha'awar Obi ya amince ya zama abokin takararsa a 2023.

"Yan arewa sun riga sun yanke hukuncin abin da zasu yi, babu tantama NNPP ce, babu wanda zai canza hakan," inji Kwankwaso.

A wani labarin kuma 'Dan majalisa da dubbannin mambobin jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC a jiha ɗaya

Ga dukkan alamu jam'iyyar PDP ta shiga babban rikici a jihar Oyo yayin da dubbannin mambobinta suka rungumi APC.

Ɗan majalisar tarayya, Muraina Ajibola, ya jagoranci mambobi sama da 18,000 sun koma APC daga PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262