Atiku, Buhari da jerin ‘Yan siyasa 10 da suka fi kowa suna a dandalin sada zumunta
- Atiku Abubakar shi ne ‘dan siyasan da ya fi kowa yawan mabiya a shafin Twitter a duk Najeriya
- Wani bincike da StatiSense tayi ya tabbatar da Atiku, Buhari da Osinbajo sun fi kowa shahara a Twitter
- Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu yana da mabiya 1.4m duk da ba ‘dan siyasa ba ne
Ga yadda abubuwan suke nan kamar yadda aka tattara:
1. Atiku Abubakar
A binciken da StatiSense tayi, duk ‘yan Najeriya babu wanda ya kai Atiku Abubakar yawan mabiya a Twitter (miliyan 4.3), shi kuwa yana bibiyar mutane 143 ne.
A Facebook akwai sama da mutane 1,106, 000 da suke bibiyar shafin ‘dan takaran shugaban kasar.
2. Muhammadu Buhari
Shi kan shi shugaban kasa Muhammadu Buhari yana bayan Atiku Abubakar ne domin mutane miliyan 4.14 suke bin shi a Twitter, amma a Facebook ya fi Atiku mutane.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
3. Yemi Osinbajo
Legit.ng Hausa ta fahimci a halin yanzu, mutane miliyan 3.84 ke bibiyar @ProfOsinbajo a Twitter. A Facebook, mataimakin shugaban kasar yana da mabiya sama da 750, 000.
4. Dino Melaye
Na hudu a jerin shi ne Sanata Dino Melaye mai mabiya kusan miliyan 3.5, shi kuwa bai bin kowa sai Dino Melaye. A Facebook, Dino bai da sa’a, yana da mabiya 1.6m.
5. Bukola Saraki
Wanda ya zo na biyar a masu farin jini da yawan mabiya a Twitter shi ne Bukola Saraki da mutane miliyan 2.88. Akwai mutum 740, 000 da ke bibiyarsa a Facebook.
Shehu Sani zuwa Peter Obi
Sauran wadanda suka cike gurbin sahun goman farko na suna a kafofin sada zumuntan sun hada da Shehu Sani, Nasir El-Rufai da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Sanata Shehu Sani yana cikin wanda suka fi kowa amfani da shafukan sada zumunta, ya yi magana fiye da sau 25, 000 a Twitter, a Facebook yana da mabiya 390, 000.
6. Shehu Sani (2.62m)
7. Nasir El-Rufai (2.12m)
8. Goodluck Jonathan (1.95m)
9. Ben Murray Bruce (1.85m)
10. Babajide Sanwo-Olu (1.7m)
11. Garba Shehu (1.42m)
12. Peter Obi (1.4m)
Za a sasanta da Wike
Ku na da labari cewa jam’iyyar PDP ta kama hanyar shawo kan sabanin da aka samu a game da wanda zai yi wa Atiku Abubakar abokin takara a zaben 2023.
Majalisar amintattu ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai yi sulhu. Da zarar Atiku Abubakar da shugaban PDP sun dawo daga kasar waje, za a soma sasantawa.
Asali: Legit.ng