Kwankwaso ya shawarci Obi da ya zama abokin takararsa, ya bayyana muhimman dalilai

Kwankwaso ya shawarci Obi da ya zama abokin takararsa, ya bayyana muhimman dalilai

  • Tsohon gwamnan jihar Kano kuma 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar NNPP ya ce Kudu maso gabas sun kware a kasuwanci kuma suna da kwazo amma an bar su a baya a siyasa
  • Kwankwaso, shugaban NNPP, ya bayyana yadda suka tattauna da jam'iyyar LP don ganin yadda zasu yi maja, amma babban kalubalen shi ne wanda zai tsaya takarar shugaban kasa
  • A cewar jigon jam'iyyar NNPP, kudu basa da gogewa a fannin siyasa, ya kamata abokinsa Peter Obi ya amshi tayinsa na zama mataimakinsa saboda wannan ita ce babbar damar kudu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rabiu Musa Kwankwaso, 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar NNPP, a ranar Asabar ya shawarci tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da ya amince da tayinsa na zama abokin tafiyarsa a zabe me karatowa.

Kwankwaso ya ce, idan Obi ya amince ya amshi tikitin takarar mataimakin shugaban kasar jam'iyyar NNPP a 2023, hakan zai bawa yankin Kudu maso gabas damar cika burinsu na mallakar mukamin shugaban kasa nan gaba.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

Premium Times ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan ya kara da cewa, amincewa ya zama abokin tafiyar da Obi ko wani daga cikin 'yan takarar shugaban kasa zai yi sanadiyyar rushewar jam'iyyarsa, NNPP.

Kwankwaso, wanda ya je jihar Gombe don rantsar da sabbin 'yan jam'iyyar da aka zaba, ya bayyana hakan ne a wata zantawa da manema labarai.

A cewar, gogewarsa a harkar siyasa na tsawon shekaru da dumbin sanin aiki, ya taimaka ga abubuwa da dama a kasar, wanda hakan ne yasa NNPP ta samu karbuwa cikin kankanin lokaci.

"Daga tattaunawar da muka yi da jam'iyyar Labour, babban kalubale shi ne wanda zai tsaya takarar shugaban kasa idan jam'iyyun suka yi maja," a cewar Kwankwaso.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Daga karshe, wasu daga cikin wakilanmu sun kawo shawarar ya kamata a saka matakai kamarsu shekaru, matakin karatu, mukaman da aka taba rikewa a baya, kwazo da sauransu," a cewar 'dan takarar shugaban kasar NNPP.

Kara karanta wannan

Yan Kudu Ba Su Yi Da Mu: Rikici Ya Barke a Jam'iyyar NRM, Mataimakin Shugaban Jam'iyya Na Kasa Da Yan Siyasan Arewa Sun Fice

"Tabbas dayan bangaren ba za su amince da haka ba. Da yawansu sun yi amanna da cewa ya kamata mulki ya koma can (Kudu maso gabas).
"Na dauki tsawon shekaru 17 ina aikin gwamnati, muna maganar shekaru 17 na tsananin jajircewa, wanda hakan ne ya ke rike NNPP a yanzu," a cewarsa.

Shugaban jam'iyyar NNPP ya ce ba yana kalubalentar mika mulki ga wani yankin kasar bane, amma dole a yi dubi da "matakai, lissafin siyasa da dabarbaru."

A cewarsa, Kudu maso gabas sun kware a harkar kasuwanci kuma suna da kwazo amma ya kamata su koyi siyasa.

"A siyasa an barsu a baya," a cewar Kwankwaso.

Ya ce yankin sun tsaida 'dan takarar shugaban kasa da mataimakansu duk daga jam'iyyar APC da PDP amma yanzu suna da dama da NNPP.

Ya ce wadanda ke cewa "koda abokina (Peter Obi) na son amincewa ya zama 'dan takarar mataimakin shugaban kasa, wasu daga cikin 'yan kudu maso gabas ba za su amince ba, wannan ba dabara bace."

Kara karanta wannan

Za mu durkusa a gaban Wike idan hakan zai sa ya ci gaba da zama a PDP, in ji Walid Jibrin

Ya ce Bola Tinubu ya yi dabarar marawa APC baya a 2015 kuma "a yau shi ne 'dan takarar shugaban kasar APC."

Kwankwaso ya ce wannan ita ce babbar dama ga kudu maso gabas da su yi maja da NNPP, "wannan ita ce babbar dama da suke da ita, idan suka rasa, hakan zai zama annoba."

Game da wanda yake son ya zama abokin tafiyarsa, Kwankwaso ya ce "Muna da zabi a NNPP na daukar abokin tafiyar a kudu wanda yafi cancanta daya daga cikin wadanda nake magana shi ne Peter Obi."

Game da yiwuwar NNPP ta kai labari a zaben 2023, Kwankwaso ya cr jam'iyyarsa na da tsari, fasali da yawan mabiya a fadin kasar da zasu iya takara gami da cin zabe.

Daga karshe, ya ce idan aka zabesa shugaban kasa a 2023, burinsa shi ne zai samar da wata kafa da matasan Najeriya zasu samu aiki, cika burinsu da karfafa a fannin ilimi da tattalin arzirki.

Kara karanta wannan

Abokin Takara: APC ta Dimauce, Tinubu ya Takaita Lalubensa a Borno, Kano, Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng