Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Wike bai gana da Tinubu ba a Faransa. Mamban BoT
- Alhaji Adamu Maina Waziri, mamba a kwamitin amintattun PDP ya musanta rahoton cewa Wike da Tinubu sun gana a Faris
- Tsohon ministan harkokin yan sandan ya ce suna tare da gwamnan Ribas, Nyesom Wike a Istanbul, Turkey kuma bai je Faransa ba
- Har yanzun ƙura bata lafa ba a babbar jam'iyyar hamayya tun bayan watsar da Wike da zaɓo gwamna Okowa a matsayin mataimakin Atiku
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Mamba a kwamitin amintattu (BoT) na jam'iyyar PDP, Alhaji Adamu Maina Waziri, ya ƙaryata rahoton da ke cewa gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya gana da ɗan takarar APC, Bola Ahmed Tinubu, a Faransa.
Daily Trust ta rahoto cewa zawarcin da manyan jiga-jigan All Progressive Congress (APC) da Labour Paryy (LP) ke yi wa Wike ya tada ƙura a jam'iyyar PDP.
Tun bayan da ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zaɓi gwamna Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa, abubuwa suka dagule wa babbar jam'iyyar hamayya.
Kwamitin da aka kafa ya bayar da shwarin a zaɓi gwamna Wike, amma Atiku ya yi watsi da su, ya ɗakko Okowa, hakan ya fusata gwamnan na Ribas da sauran yan tawagarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake martani kan zancen ganawar Tinubu da Wike, Maina ya ce ya kasance tare da gwamnan Ribas ranar Laraba a birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya.
Maina, tsohon ministan harkokin yan saanda ya ce:
"Gwamna Wike ya taho kai tsaye zuwa Birnin Istanbul na kasar Turkiyya, bai je Faransa ba kamar yadda ake yaɗa wa. Wannan kaɗai ya isa yin fatali da Farfagandar APC ta bakin Igbokwe."
"Labarin ƙaryace da babu ɗugon gaskiya wanda jam'iyya mai mulki da ke tangal-tangal ta kirkira don wata manufa daban."
Meya kai su birnin Istanbul?
Yayin da aka jefa masa tambayar ko wace manufa suka tafi Istanbul don su cimmawa, Maina ya amsa da cewa:
"Meye damuwar ku da abinda muka sa a gaba? Mun zo mu sha iska ne bayan babban taron mu. Eh gaskiya ne, a matsayin ɗan siyasa, a ko ina na je na kan saka siyasa ta."
A wani labarin kuma Danbarwa ta ɓarke a majalisar dokokin jiha a arewa, mambobi 22 sun ɓalle, sun nemi kakaki ya yi murabus
Rikicin shugabanci ya kunno kai a majalisar dokokin jihar Bauchi yayin da mambobi 22 suka nemi duk me rike da ofishi ya yi murabus.
Shugaban mambobin 22 kuma mataimakin shugban masu rinj a ye ya ce su aje aiki ko kuma su tsige su kowane lokaci ɗaga yanzu.
Asali: Legit.ng