Jiga-Jigan Jam'iyyar APC Masu Yawa Sun Koma ADC a Sokoto

Jiga-Jigan Jam'iyyar APC Masu Yawa Sun Koma ADC a Sokoto

  • Wasu jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Sokoto sun fice daga jam'iyyar sun koma African Democratic Party, ADC
  • Dumebi Kachikwu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC ne ya tarbe su a ranar Alhamis a Sokoton yayin da ya taho kaddamar da sakatariyar jam'iyyar a jihar
  • Kachikwu ya musu alkawarin cewa jam'iyyar ADC ba za ta nuna musu wariyya ba kuma ya yi wa mutanen Sokoto alkawarin cewa ba za su basu kunya ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Sokoto - Dubban magoya baya ne a ranar Alhamis suka fito domin tarbar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress, ADC, Dumebi Kachikwu a Sokoto.

Kachikwu da wasu manyan shugabannin jam'iyyar na ADC sun dira Sokoto ne domin kaddamar da sabuwar sakatariyar jam'iyyar tare da karbar daruruwan sabbin mambobi da suka baro jam'iyyar APC zuwa ADC.

Kara karanta wannan

Yan Kudu Ba Su Yi Da Mu: Rikici Ya Barke a Jam'iyyar NRM, Mataimakin Shugaban Jam'iyya Na Kasa Da Yan Siyasan Arewa Sun Fice

Tambarin Jam'iyyar ADC.
Jiga-Jigan Jam'iyyar APC Masu Yawa Sun Koma ADC a Sokoto. Hoto: @nigeriantribune.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dan takarar shugaban kasa jam'iyyar na ADC a zaben 2023 ya tarbi jiga-jigan jam'iyyar APC fiye da 120 da suka fice suka dawo ADC, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kachikwu ya shaida wa wadanda suka sauya shekan cewa ADC ta yi imani da kasa daya dunkulalliya, cigaban yan Najeriya baki daya, girmama doka da kauna sune abubuwan da suka hada kan yan Najeriya.

Ba za mu bawa Sakkwatawa kunya ba - Kachikwu

Ya ce sabuwar sakatariyar za ta zama alama na fatan samun alheri a nan gaba, yana mai cewa ADC ba za ta bawa mutanen Sokoto kunya ba.

Kachikwu ya fada wa magoya bayan jam'iyyar su rungumi ADC a matsayin jam'iyya na dukkan yan Najeriya, a yayin da ya basu tabbacin cewa ba bu wariya a tsakanin mambobi a dukkan lokuta.

Kara karanta wannan

Sokoto: 'Yan Takarar Gwamna 2, 'Yan Majalisa da Mabiya 3,000 na APC Sun Koma PDP

Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba

A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi ta Yamma a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.

Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel