Har yanzu ana ta yunkurin hada-kan Obi da Kwankwaso, maganar na nan inji NNPP, LP
- Kokarin da ake yi na samun hadin-kai tsakanin Labour Party da New Nigeria Peoples Party na nan
- Jagororin wadannan jam’iyyu sun tabbatar da cewa su na cigaba da magana domin a bullowa 2023
- Dr. Agbo Major da Dr. Yunusa Tanko duk sun nuna a shirye suke da a hadu domin a ceto al’umma
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Maganar da ake yi na samun hadin-kai tsakanin jam’iyyar Labour Party da New Nigeria Peoples Party watau NNPP a zaben 2023 ba ta shiriri ce ba.
Rahoton da Vanguard ta fitar a safiyar Juma’a, 1 ga watan Yuli 2022, ya tabbatar da cewa wadannan jam’iyyun hamayya su na neman su dunkule tare.
Babban jami’in hulda da jama’a na NC Front, Yunusa Tanko da sakataren yada labarai na NNPP, Agbo Major, duk sun tabbatar da wannan da aka yi hira da su.
Dr. Yunusa Tanko ya shaidawa manema labarai cewa takarar Peter Obi ta gawura, har abin ya sha gaban jam’iyyar LP domin mutane da-dama su amsa kiransa.
Kowa ya bi Peter Obi - NC Front
A cewar Tanko, ‘Yan Najeriya daga bangarori dabam-dabam da addinai da magoya bayan jam’iyyun siyasa iri-iri, su na tare da Obi, za su zabe shi a 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ji Tanko yana bayanin muhimmancin a hada-kai domin ayi waje da mulkin APC da na PDP domin a halin da ake ciki, babu wani yanki ko kabila da ta tsira.
“Har yanzu Labour Party, wanda ita ce jam’iyyar da NC Front, #EndSARS da sauran kungiyoyi masu zaman kansu suka zaba, ta na tattaunawa da NNPP.”
“A shirye mu ke da mu shiga yarjejeniyar hadin-kai domin ceto kasarmu daga wahalar da ake ciki, matsalar tsaro, da rashin aikin da al’umma ke fuskanta.”
NNPP sun ce ana ta magana da LP
A bangaren NNPP, Dr. Agbo Major ya tabbatar da cewa su na cigaba da magana da jam’iyyar LP da nufin ganin yadda za su shiga takara tare a zaben 2023.
“Akwai watanni kafin zaben 2023, jagororinmu su na tattaunawa domin duk mun yarda cewa mafi yawan ‘yan Najeriya sun gaji da gwamnatin APC mai-ci.”
“Mu na bukatar juna domin mu ceto kasar nan. Ana tattaunawa, kuma zan iya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa idan an cin ma matsaya, to za a sanar da su.”-
- Dr. Agbo Major
Hadin-kan zai yi wahala...
Legit.ng Hausa ta yi magana da wani daga cikin ‘yan darikar Kwankwasiyya wanda suke tare da Rabiu Kwankwaso, ya shaida mana zai yi wahala a ci nasara.
‘Dan siyasar ya ce dunkulewar NNPP da LP zai yi wahala domin ana maganar cewa sai dai Kwankwaso ya karbi tikitin mataimaki, Peter Obi ya yi takara.
Shinkafa da Wake a jihar Imo
Dazu kuma aka ji labari wani jagora a jam’iyyar APC ya yi watsi da batun sak, ya ce shinkafa da wake zai yi a 2023 tun da har aka ba Asiwaju Bola Tinubu tikiti
Tsohon mataimakin gwamnan Imo da suka yi fada da Rochas Okorocha, Jude Agabos yace zai zabi Hope Uzodinma na APC da Peter Obi na jam’iyyar LP a 2023.
Asali: Legit.ng