Babbar magana: An yi dirama a majalisa, tsakanin Ahmad Lawan da Okorocha
- An samu 'yar tsama da sabani tsakanin shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da Sanata Rochas Okorocha
- Hargitsin ya faru ne daidai lokacin da zauren majalisa ke tambayoyin tantance wasu mutum da Buhari ya zaba su zama ministoci
- A rahoton da muka samu, an ga lokacin da lamarin ya faru, da kuma yadda diramar ta kare cikin sauki
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Dan karamin rikici ya barke a zauren majalisa lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya kashe na’urar magana ga Sanata Rochas Okorocha (APC: Imo ta Yamma) yayin tantance sunayen ministoci.
Matakin na Lawan ya biyo bayan yunkurin da Okorocha ya yi na yiwa daya daga cikin wadanda aka nada a matsayin minista, Goodluck Nana Opiah, mai wakiltar jihar Imo wasu tambayoyi, rahoton The Guardian.
Ciki fushi, tsohon gwamnan na Imo ya bukaci sanin dalilin da ya sa Lawan ya baiwa wani dan majalisa, Francis Onyewuchi Ezennwa damar yin magana amma shi aka hana shi magana.
Da yake fayyace batun Okorocha na yin tambayoyi barkatai ga ministan, Shugaban Majalisar Dattawa ya gargade shi game da saba yarjejeniyar da aka cimma a zaman sirri na majalisar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jim kadan bayan tantance shi, Opiah ya shaida wa manema labarai cewa babu ‘mummunan abu’ a tsakaninsa da Sanatan, inda ya nanata cewa, tsohon gwamnan yana da hali mai kyau.
Opiah ya kasance tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Imo kuma mamba mai wakiltar mazabar Ohaji/Egbema, Oguta da Oru ta yamma a majalisar wakilai.
A wani bidiyon da muka samo daga Viable Tv, an ga lokacin da hargitsin ya faru tsakanin Ahmad Lawan da Rochas Okorocha.
Kalli bidiyon:
Majalisar Dattawa Tana Tantance Ministoci 7 da Buhari ya Mika Sunayensu
A wani labarin, majalisar dattawa ta fara tantance zababbun sabbin ministoci bakwai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike musu da shi.
Wadanda aka zaban sun samu rakiyar 'yan uwansu, abokan arziki da magoya baya, ana tantance su daya bayan daya a yayin zaman majalisar, Daily Trust ta ruwaito.
Buhari a wasikar da ya aike a ranar 15 ga watan Yunin 2022, ya bukaci majalisar da ta tabbatar da su a matsayin sabbin ministocin da zasu maye gurbin bakwai da suka yi murabus.
Asali: Legit.ng