Gwamnan PDP Ortom: Har yanzu Allah bai yarje min na goyi bayan Atiku ba

Gwamnan PDP Ortom: Har yanzu Allah bai yarje min na goyi bayan Atiku ba

  • Gwamnan Benue ya bayyana matsayarsa game da goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsu ta PDP
  • Ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin, inda ya yi bayanai masu daukar hankali
  • Ya ce, ya zuwa yanzu dai ba ya goyon bayan Atiku, amma watakila Allah ya amince masa ya karbi hakan a gaba

Benue - Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue, ya ce yana “azumi da addu’a” domin neman dace daga Allah kafin ya yanke shawarar goyon bayan Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin ta Arise a ranar Laraba, The Cable ta ruwaito.

Matsayar Ortom kan takarar Atiku
Gwamnan PDP Ortom: Har yanzu Allah bai yarje min na goyi bayan Atiku ba | Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

A watan Mayu, Atiku ya yi fatali da Nyesom Wike, gwamnan Rivers, inda ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na PDP.

Kara karanta wannan

Za mu durkusa a gaban Wike idan hakan zai sa ya ci gaba da zama a PDP, in ji Walid Jibrin

Daga nan sai dan takarar ya bayyana Ifeanyi Okowa, gwamnan Delta, a matsayin abokin takararsa duk da cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC) ya ba da Wike matsayin abokin takarar Atiku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin dai ya haifar da cece-kuce a tsakanin duk wadanda abin ya shafa da kuma magoya bayansu.

Da yake magana game da hakan, Ortom ya yaba wa Wike a matsayin "wanda ya tsaya wa jam'iyyar kuma ya tabbatar da cewa abubuwa sun yi aiki".

Ya kara da cewa "wasu daga cikinmu sun yi imani da shi" a matsayin mafi kyawun zabi na jam'iyyar ga dan takarar mataimakin shugaban kasa.

A wani zubin, ya bayyana cewa zai marawa Atiku baya ne kawai idan Allah ya ba shi dama.

Atiku ya ci fuskar Wike, inji Ortom

A bangare guda kuma, Ortom ya ce Atiku ya ci zarafin Wike ta hanyar tura mutane su kira shi, Pulse.ng ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An yi kus-kus: Abin da Bola Tinubu ya shaida wa sanatocin APC a wata ganawar sirri

Ortom ya ce:

“Ai cin fuska ne ga Atiku Abubakar ya tura mutane zuwa ga babban dan gwagwarmaya kamar Wike.
“Atiku ya bata wa Wike rai. Cin fuska ne Atiku ya tura mutane su kira Wike.
"Atiku da shugabannin jam'iyyar a dukkan matakai dole ne su ziyarce shi, Wike babban ginshiki ne a PDP.
"Me yasa Atiku ba zai iya ziyartar Wike da kansa ba?"

2023: Tashin hankali a PDP yayin da mambobi 10,000 suka tsallake zuwa APC

A wani labarin, akalla mambobin jam’iyyar PDP 10,000 ne aka bayyana cewa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Osun a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa, an yi wannan biki na sauya sheka ne a filin shakatawa na Nelson Mandela da ke Osogbo, babban birnin jihar.

Legit.ng ta tattaro cewa Hon Wale Ojo, shugaban tsagin PDP na jihar, da Hon Albert Adeogun, dan takarar mataimakin gwamnan PDP a zaben 2018 a Osun, na daga cikin wadanda suka fice daga PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike ya fadi dalilin da ya sa 'Dan takaran NNPP, Kwankwaso ya ziyarce shi a gida

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.