Sauya Sheka: Fusatattun Sanatocin APC Sun Gana da Buhari a Aso Rock

Sauya Sheka: Fusatattun Sanatocin APC Sun Gana da Buhari a Aso Rock

  • Fusatattun sanatocin APC har 22 da suka sha alwashin barin jam'iyya baki daya sun samu ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Sanata Orji Uzor Kalu, bulaliyar majalisar dattawa ne ya jagoranci sanatocin zuwa gaban Buhari inda suka tattauna ranar Talata
  • Kamar yadda shugaban kasan ya bayyana, sauya shekarsu babbar barazana ce ga jam'iyyar dake da rinjaye a majalisar dattawa

Abuja - Wasu fusatattun sanatocin dake jam'iyyar APC sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja a ranar Talata.

Sanatocin da suka kai wurin 22, sun sha alwashin barin jam'iyyar saboda sakamakon zabukan fidda gwani na jihohinsu da aka yi kafin zaben 2023.

Shugaban tawagar sanatocin shine Santa Orji Uzoe Kalu, ya ce 'yan majaliar basu ji dadin abinda ya faru ba ko kadan, Channels TV ta ruwaito

Kara karanta wannan

'A haife shi a 1958, ya fara makaranta 1959?' Sabbin matsaloli da suka taso kan takardun sabon shugaban Alkalai

Sanatocin APC tare da Buhari
Sauya Sheka: Fusatattun Sanatocin APC Sun Gana da Buhari a Aso Rock. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

A yayin jawabi a taron, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga sanatocin da hakura da tunanin barin jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatoci masu yawa na jam'iyyar APC sun sauya sheka a cikin kwanakin nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace sauya shekar babba barazana ce ga APC wacce ke da rinjaye a majalisar dattawa.

Bayan taron, Kalu yace fusatattun sanatocin sun fasa sauya sheka ko barin jam'iyyar baki daya.

“A safiyar yau, na jagoranci fusatattun sanatocin jam'iyyar APC 22 zuwa gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR," Kalu, bulaliyar majalisa ta tara yace a wata takarda.
"Mun samu ganawa cike da nasara da shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma batun sauya sheka daga jam'iyyarmu duk ya lafa," yace.

Zaben 2023: Jerin Sanatocin APC da Suka Sauya Sheka Zuwa PDP da Wasu Jam'iyyu

A wani labari na daban, yayin da ake jiran zuwan ranar zaben shekarar 2023, wasu sanatotin jam'iyya mai mulki ta APC sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP da sauran jam'iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Mutanen Tinubu sun fara zawarcin jam’iyyun da basu da yan takarar shugaban kasa

Yawancin idan ba duka wadanda suka sha kaye a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC sun sauya sheka bayan gaza samun tikitin tsayawa takara domin cigaba da tabbata a madafun iko ko tsayawa takarar gwamna a zaben shekarar 2023.

A kalla sanatoci bakwai na jam'iyya mai mulki ta APC sun sauya sheka zuwa ko dai PDP ko kuma wata jam'iyyar adawa kafin zabe mai karatowa na shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng