Yanzun Nan: Wani karin sanatan APC ya bi sahu, ya fice daga jam'iyyar
- An sake samun karin wani Sanatan APC da ya tabbatar da barin jam'iyyar duk da yunkurin sasanci da ɗinke ɓarakar cikin gida
- Sanatan mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta arewa, Godiya Akwashiki, ya ce mutanen mazaɓarsa sun jima suna matsa masa lamba
- Ya bayyana canza jerin sunayen Deleget a wurin zaɓen fidda gwani a matsayin dalilinsa na barin APC
Nasarawa - Yayin da jam'iyyar APC ke kokarin ɗinke barakar da ke kwashe mata Mambobi a majalisar Dattawa, Sanata Godiya Akwashiki, mai wakiltar mazaɓar Nasarawa da arewa ya fice daga jam'iyya mai mulki.
Daily Trust ta ruwaito cewa Akwashiki ya sanar murabus daga APC ne a wurin kaddamar da aikin gina hanyar Nassarawa Eggon/ Galle, da ke ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon, ranar Litinin.
Ɗan majalisar tarayya ya kafa hujja da zargin jirkita sunayen Deleget a matsayin dalilin da ya sa ya ɗauki matakin ficewa daga jam'iyyar.
Sanatan ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Dukkan ku kuna da masaniyar abinda ya wakana a wurin taron zaɓen fidda gwanin APC wanda ya gudana a Akwanga. Na janye daga takara saboda jam'iyya ta canza Deleget."
"Kun matsamun lamba kan na fita daga jam'iyyar kuma yau na amsa kiran ku na barin APC domin sake ɗaura ɗamar neman tazarce a zaɓe na gaba."
"Nan da awanni 72 masu zuwa zaku san sabuwar jam'iyyar da zan koma kuma dukkan mu, ni da ku zamu sauya sheƙa zuwa jam'iyyar."
Shin meye matsalar da ke damun Sanatocin APC?
Wannan na zuwa nw bayan babban jigon APC kuma tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi gargaɗin cewa akwai karin Sanatovi sama da 20 da ka iya barin APC.
A cewarsa, suna ɗaukar matakin sauya sheƙan ne saboda gazawar jam'iyya na ba su tikitin sake tsayawa takara a babban zaɓen 2023 da ke tafe.
A wani labarin kuma Gwamna Wike, Tambuwal, Diri da sauran jiga-jigan da zasu jagoranci Kanfen na PDP a jihar Osun
Yayin da ake gab da fita fafata zaɓe n gwamnan Osun, jam'iyyar PDP ta kafa tawagar yaƙin neman zaɓen ɗan takararta.
Gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, ne zai jagoranci tawagar yayin da gwamnoni 11 zasu mara masa baya a matsayin mambobi.
Asali: Legit.ng