Sokoto: 'Yan Takarar Gwamna 2, 'Yan Majalisa da Mabiya 3,000 na APC Sun Koma PDP
- APC ta yi rashin mabiya har 3000, 'yan takarar gwamna biyu, 'dan majalisar tarayya, a jihar Sokoto inda suka koma babbar jam'iyyar adawa ta PDP
- Yayin jawabi a filin wasa na Ginginya inda aka yi bikin sauya shekar, shugaban wadanda suka bar APC kuma 'dan majalisar da ke wakiltar mazabar Illela ya ce sun yanke shawarar yin hakan ne take yanke
- 'Yan siyasan sun koka da halin da jam'iyyar ta shiga a fadin jijhar inda suka ce mutum daya ke juya ta tare da yin duk abinda ya ga dama ba tare da ya duba matsalar wasu ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Sokoto - APC ta rasa magoya baya 3,000, 'yan takarar gwamna biyu, wani 'dan takarar majalisar tarayya ga PDP a jihar Sakkwoto.
Yayin zantawa a filin wasa na Ginginya wajen da suka yi bikin sauya shekar, shugaban masu sauya shekar da wani 'dan majalisar da ke wakiltar mazabar tarayya ta Illela/ Gwadabawa Abdullahi Balarabe Salame, ya ce sun yanke shawarar ne a lokaci guda.
Salame wanda tsohon 'dan takarar gwamna ne a jam'iyyar APC ya janye daga takarar ne ana saura lokaci kalilan kafin fara zaben fidda gwanin a Sakkwoto, wanda tsohon mataimakin gwamna Ahmad Aliyu Sakkwoto ya zama zakaran gwajin dafi.
"APC a jihar Sakkwoto ta zama jam'iyyar mutum daya wanda ke wasa da Ubangiji ba tare da sanin bishiya daya bata daji ba" a cewar Salame.
Vanguard ta ruwaito cewa, Kadarin siyasar APC ya rushe zuwa PDP don tabbatar da PDP tayi gagarumar nasara a zaben 2023.
Ta bangarensa, gwamnan jihar Sakkwoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana yadda ya shiga cikin matsanancin farin ciki da tarbar wandanda suka sauya shekar zuwa PDP.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan ya cigaba da bayyana yadda suka ga alamar haske tare da yanke shawarar bin shi, inda ya ce APC na neman agaji jiran mutuwa kawai ta ke.
"Bari in tambayeku, waye mataimakin 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, amsar shi ne babu, suna kiransa da na wucin gadi.
"APC ta shiga rudani tare da ikirarin za su je ga matsayar abokin tafiyar'dan takarar shugaban kasar zaben 2023 lamarin da ko 'yan Najeriya na iya kai matsaya" a cewar Tambuwal.
Yayin jawabi, mataimakin 'dan takarar jam'iyyar PDP kuma gwamnan jihar Delta Sen Authur Ifeanyi Okowa ya jinjinawa wadanda suka sauya shekar bisa daukar matakin da ya dace.
"Bari in tambayeku, da gwamnati ta damu da halin da kasar za ta shiga a gaba da tuni sun daidaita da ASUU kafin yanzu," a cewarsa.
APC ta shiga Tasku a Kebbi, Sanatocin Jam'iyyar 2, da Wasu Mutum 6 Sun Koma PDP
A wani labari na daban, jam'iyyar APC a jihar Kebbi ta fara shiga wani hali yayin da ta rasa 'yan majalisar tarayya biyar da 'yan majalisar jiha uku inda suka koma babbar jam'iyyar adawa ta PDP.
Sauya shekar da 'yan jam'iyyar suka yi zuwa PDP ya fara ne byan kammala zaben fidda gwamnin jam'iyyar bayan wadanda suka sauya shekar sun caccaki yanayin zaben fidda gwani da aka yi a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Sanata Adamu Aliero mai wakiltar mazabar Kebbi ta tsakiya, shugaban majalisar dattawa, Dr. Yahaya Abdullahi mai wakiltar mazabar Kebbi ta arewa tare da mamban majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kalogo/Bunza a tarayya su ne na farko da suka sanar da sauya shekarsu zuwa PDP.
Asali: Legit.ng