Da Dumi-Ɗumi: Ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ya tafi ƙasar Faransa
- Tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya tafi ƙasar Faransa don cigaba da neman shawari bayan gana wa da Buhari
- Mai magana da yawun jigon APC na ƙasa, Tunde Rahman, ya ce Tinubu zai halarci wasu taruka masu muhimmanci a birnin Farisa
- An bayyana Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na APC bayan lashe zaɓen fidda gwani
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressive Congress wato APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fice daga Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Jagoran APC na ƙasa ya nufi ƙasar Faransa bayan gana wa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa Aso Villa dake birnin tarayya Abuja, da safiyar Litinin.
Mai magana da yawun ɗan takarar na APC, Tunde Rahman, wanda ya sanar da lamarin, bai bayyana adadin lokacin da Bola Tinubu zai kwashe yayin tafiyar ba.
Amma a sanarwan, Rahman ya tabbatar da cewa ana tsammanin Bola Tinubu zai dawo gida Najeriya nan ba da jimawa ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce:
"Ya tafi birnin Farisa na ƙasar Faransa domin halartar wasu taruka masu matuƙar muhimmanci."
Leadership ta rahoto cewa kwana ɗaya kafin tafiyarsa, Tinubu, ya halarci kaddamar da wani littafi mai suna, "Mista Kakakin majalisa," da buɗe shirin ba da horo kan ayyukan majalisar dokoki duk a wani ɓangare na bikin cika shekara 60 na kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.
A ranar 8 ga watan Yuni, aka ayyana Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a zaɓen 2023 da ke tafe bayan samun nasara a babban taron zaɓem fidda gwani na jam'iyyar wanda ya gudana a Eagle Square.
Bayan kammala zaɓen, tsohon gwamnan jihar Legas ya kai ziyarar godiya da kuma neman sulhu ga sauran yan takarar da suka fafata da shi ciki har da waɗanda suka janye masa.
Gwamnan APC ya ba yan bindiga wa'adi
A wani labarin kuma Gwamna Uzodinma ya ba yan bindiga kwanaki 10 su aje makamansu ko su funkanci ruwan wuta
Yayin da gwamnan ke shirin karɓan bakuncin shugaban ƙasa Buhari, ya shawarci yan ta'adda su gaggauta barin dazukan jihar Imo.
Hope Uzodinma, ya ce jiharsa zata karɓi bakuncin bikin shekara-shekara n a hukumomin tsaro wanda za'a fara daga 30 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng