Bola Tinubu ya yi watsi da batun rashin takardu, ya yi magana a kan neman abokin takara

Bola Tinubu ya yi watsi da batun rashin takardu, ya yi magana a kan neman abokin takara

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya halarci bikin taya Femi Gbajabiamila murnar cika shekara 60 a Abuja
  • Bola Tinubu ya bayyana cewa har yanzu dai yana neman ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa
  • Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya nuna zai iya zabawa ‘dan takaran wanda zai rike masa tikiti a 2023

Abuja - Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa har yanzu yana neman wanda zai zama abokin takararsa ne a zaben shugaban kasa da za ayi a 2023.

Daily Trust ta rahoto cewa ‘dan takarar ya yi watsi da surutan da jama’a suke yi, har da ana zargin bai yi makaranta ba saboda takardun da ya gabatarwa INEC.

Da yake bayani a wajen taya shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, murnar cika shekara 60, Tinubu ya tabo batun takarar 2023.

Kara karanta wannan

2023: Mutane za su gamsu idan su ka ji wanda Tinubu zai tafi da shi inji Jigon APC

Har aka gama wannan taro, Asiwaju Bola Tinubu bai yi magana a kan zargin da ake yi masa na cewa bai halarci makarantar boko kamar yadda yake ikirari ba.

‘Dan siyasar yake cewa har yanzu ana neman ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa ne a APC.

Rahoton ya ce a wajen wannan taron biki, Bola Tinubu ya yabawa Gbajabiamila a kan yadda alakarsa da mataimakinsa, Hon. Ahmed Wase ta ke tafiya sumul.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bola Tinubu
Femi Gbajabiamila da Bola Tinubu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Alakar Gbajabiamila da Wase

A cewar ‘dan siyasar, ya kamata har shi karon kansa ya dauki darasi daga wannan dangataka. Bugu da kari, Tinubu ya yabi kokarin da Gbajabiamila ya yi masa.

‘Dan takarar shugaban kasar yace sai a nan gaba zai bada labarin gudumuwar da shugaban majalisar wakilan na Najeriya ya ba shi a zaben tsaida gwani na APC.

Kara karanta wannan

Jam'iyya Zata Maka Tinubu a Kotu Kan Bayanan Bogi a Takardun Karatunsa

“Zan iya ganin Wase yana zaune shi ma, ka cika tambarin zaman lafiya, gaskiya da abin dogara. Nagode dukkanku, ba ku bada kunya ba.”
“Zan bukaci in koyi darasi a wurinku, yadda ku ka yi aiki tare domin har yanzu ina neman wanda zai zama mani abokin takara ne a zabe.”

- Bola Tinubu

Zan ba Tinubu abokin tafiya - Gbajabiamila

Da yake na shi jawabin, Gbajabiamila ya yi alkawarin zai zabawa Mai gidan na sa wanda zai rike masa tikiti a 2023, kuma zai zama wanda zai ji dadin aiki da shi.

An rahoto 'dan majalisar yana magana cikin wasa, yake cewa ba kyauta zai yi aikin zakulo wanda ya dace ya zama 'dan takarar mataimakin shugaban kasa ba.

Kwankwaso ya dawo APC

Ku na da labari mataimakin Kakakin jam’iyyar APC na kasa ya ce har yanzu Rabiu Kwankwaso bai makara ya dawo APC ba, domin a nan ne zai iya mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Jerin zargin rashin gaskiya da ke jikin ‘Yan takaran 2023, Atiku Abubakar da Bola Tinubu

Yakubu Ajaka ya yi bayanin makomar Atiku Abubakar, NNPP da Peter Obi, ya ce APC za ta so ta sakawa Sanata Kwankwaso abin da ya yi mata a lokacin zaben 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng