Zaben 2023: Jerin Sanatocin APC da Suka Sauya Sheka Zuwa PDP da Wasu Jam'iyyu

Zaben 2023: Jerin Sanatocin APC da Suka Sauya Sheka Zuwa PDP da Wasu Jam'iyyu

Yayin da ake jiran zuwan ranar zaben shekarar 2023, wasu sanatotin jam'iyya mai mulki ta APC sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP da sauran jam'iyyun adawa.

Yawancin idan ba duka wadanda suka sha kaye a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC sun sauya sheka bayan gaza samun tikitin tsayawa takara domin cigaba da tabbata a madafun iko ko tsayawa takarar gwamna a zaben shekarar 2023.

Majalisar Dattawan Najeriya
Zaben 2023: Jerin Sanatocin APC da Suka Sauya Sheka Zuwa PDP da Wasu Jam'iyyu. Hoto daga Nigerian Senate
Asali: UGC

A kalla sanatoci bakwai na jam'iyya mai mulki ta APC sun sauya sheka zuwa ko dai PDP ko kuma wata jam'iyyar adawa kafin zabe mai karatowa na shekarar 2023.

Hakan yasa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu ya gana da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da sauran sanatocin APC a ranar Laraba, 22 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Jigon APC: Sanatocin Mu 22 Suna Barazanar Komawa Jam'iyyar PDP, Dole Mu Dauki Mataki

Bayan ganawar, Adamu ya bayyana damuwarsa bisa yadda ake ta ficewa daga jam'iyyar, duk da hakan yana da nasaba da karatowar lokacin zabe, yayin da kasar ta saba da fuskantar duk ire-iren wadannan kalubalen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga jerin sunayen sanatocin da suka sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyoyin adawa:

  1. Ibrahim Shekarau na jihar Kano
  2. Yahaya Abdullahi na jihar Kebbi
  3. Adamu Aliero na jihar Kebbi
  4. Dauda Jika na jihar Bauchi
  5. Ahmad Babba Kaita na jihar Katsina
  6. Lawal Yahaya Gumau na jihar Bauchi
  7. Francis Alimekhena na jihar Edo.

Sanatocin APC 22 da ke shirin ficewa daga jam'iyyar

Fani Kayode ya bayyana yadda a halin yanzu wasu sanatocin APC 22 ke shirin ficewa daga jam'iyya mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Tsohon ministan sufurin jiregen saman kuma jagora a jam'iyyar ya bayyana yadda shirin sauya shekara ke da nasaba da yadda aka hana sanatocin tikitin tsayawa takara a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Adamu Da Sanatocin APC Sunyi Taro, An Dauki Matakan Dakile Ficewar Mambobin Jam'iyyar

Yayin bayyana alhininsa bisa yadda ake tururuwar ficewa daga jam'iyyar, Fani Kayode a wata wallafa da ya fitar a shafinsa na Twitter ranar Laraba ya ce dole ne a yi wani abu don shawo kan lamarin.

"Sanatoci 22 na barazanar ficewa daga jam'iyyar zuwa PDP saboda an hana su tikitin tsayawa takarar domin dawowa majalisar dattawa.
"Wannan lamarin ya yi kamari kuma dole ne a yi wani abu don shawo kan lamarin. Mutane da dama sun shiga damuwa, sannan muna kira ga shugaban jam'iyyar na kasa da magatakarda jam'iyyar da su tuntubesu. Ba za mu iya jure rasa su ba," a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng