2023: 'Dan Takarar Gwamna Ya Zakulo Zukekiyar Jarumar Fim a Matsayin Mataimakiyarsa

2023: 'Dan Takarar Gwamna Ya Zakulo Zukekiyar Jarumar Fim a Matsayin Mataimakiyarsa

  • 'Dan takarar kujerar gwamnan jihar Ribas karkashin jam'iyyar ADC, Mista Tonte Ibraye ya zabo jaruma Tonto Dikeh matsayin abokiyar tafiyarsa
  • Kamar yadda jarumar fina-finan kudancin Najeriya ta sanar a shafinta na Instagram, tace zasu Inganta rayuwar matasa da mata
  • Ta mika godiya ga 'dan takarar tare da bayyana cewa kananan kasuwanci zasu habaka yayin da zasu ceto jihar Ribas a 2023

Ribas - 'Dan takarar kujerar gwamnan jihar Ribas karkashin jam'iyyar ADC, Mista Tonte Ibraye, ya sanar da sunan jarumar fina-finan kudu, Tonto Dikeh, a matsayin mataimakiyarsa a zaben gwamnoni na 2023 a jihar.

Jarumar ta garzaya shafinta na Instagram a ranar Juma'a inda ta sanar da labarin tare da mika godiyarta ga 'dan takarar kan zabenta da yayi.

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt

'Dan Takarar Gwamna Da Mataimakiyarsa
2023: 'Dan Takarar Gwamna Ya Zakulo Zukekiyar Jarumar Fim a Matsayin Mataimakiyarsa. Hoto daga Vanguardngrnews.com
Asali: UGC
Ta rubuta, "Ina godiya ga Mista Tonte Ibraye, 'dan takarar gwamnan jihar Ribas na jam'iyyar ADC kan zabena da yayi a matsayin abokiyar tafiyarsa.
"Za mu tabbatar da Inganta rayuwar matarsa, janyo mata cikin tsarin gwamnati, habaka kananan kasuwanci da Inganta cibiyoyinmu na gargajiya ta yadda zasu kawo cigaba ga jama'ar jihar Ribas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ina farin cikin kasancewa mamba #KudirinCetoRibas2023. Ku tabbatar kun mallaki katin zabenku tare da shiga wannan tafiya."

Shugaba Buhari ya yi wa Obasanjo shagube, yace ba zai nemi ya sake zarcewa a mulki ba

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa ba zai nemi karin wa’adi idan lokacinsa ya cika ba, ya jaddada barinsa mulki a 2023.

Da yake jawabi a wajen taron CHOGM na kasashen renon Birtaniya da ake yi a Kigiali, kasar Rwanda, Muhammadu Buhari ya ce ya gama yin takara.

Kara karanta wannan

Lauyoyi: Maye Gurbin Machina da Ahmad Lawan Ya Fallasa Goyon Bayan Rashin Bin Dokar APC

Daily Trust ta rahoto Buhari a tattaunawarsa da Firayin Ministan Birtaniya, Boris Johnson yana cewa wanda ya nemi ya zarce a karo na uku bai ji dadi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng