Da Ɗumi-Dumi: Sanatocin PDP sun gana da gwamna Wike a Patakwal

Da Ɗumi-Dumi: Sanatocin PDP sun gana da gwamna Wike a Patakwal

  • Sanatocin jam'iyyar PDP sun gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a gidansa da ke Patakwal, babban birnin jihar ranar Alhamis
  • Sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar Dattawa, Sanata Philip Tanimu Aduda na cikin waɗan da suka halarci taron
  • Babu ɗayan mahalarta taron da ya gaya wa manema labarai abinda suka tattauna da gwamnan bayan sun fito

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Shugabannin mambobin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar dattawa, ranar Alhamis, sun gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike.

Leadership ta ruwaito cewa Sanatocin babbar jam'iyyar hamayyan sun gudanar da taron a sirrance a gidan Wike dake Patakwal, babban birnin jihar Ribas.

Sanatocin PDP da Wike.
Da Ɗumi-Dumi: Sanatocin PDP sun gana da gwamna Wike a Patakwal Hoto: Marshal Obuzor/facebook
Asali: Facebook

Daga cikin waɗan da suka halarci taron sirrin wanda ya shafe awanni sama da biyu, sun haɗa da sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Philip Tanimu Aduda da Sanata Chukwuka Utazi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kwanaki kalilan bayan ficewa daga PDP, Tsohon Minista ya sa labule da gwamna Wike

Haka zalika sauran waɗan sa suka samu halartar ganawar sune, mataimakin shugaban marasa rinjaye, Sanata Shuaibu Lau, Sanata Ɗanjuma La'ah, da kuma Sanata Barry Mpigi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Me suka tattauna a wurin ganawar?

Sai dai baki ɗaya mahalarta taron, babu wanda ya faɗa wa manema labarai babban maƙasudin taron da kuma abubuwan da aka cimma a wurin.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa taron ya biyo bayan ziyarar da tsohon ministan harkokin Neja Delta, Orubebe, ya kai wa Wike har gida yau Alhamis

Orubebe ya sanar da ficewarsa daga PDP kawanaki kaɗan da suka gabata, a wani yunkuri na nuna adawarsa da matakin jam'iyyar na tsayar da ɗan arewa takarar shugaban ƙasa.

A wani labarin kuma Kwanaki kalilan bayan ficewa daga PDP, Tsohon Minista ya sa labule da gwamna Wike

Kwanaki kaɗan bayan ya yi murabus daga PDP, Tsohon ministan Neja Delta, Chief Orubebe, ya gana da gwamnan Ribas, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu a birnin Landan ta hana Ike Ekweremadu beli, tace a garkameshi a Kurkuku

Taron mutanen biyu ya gudana ne a gidan Wike dake Patakwal, babban birnin jihar Ribas kuma a sirrance, ba su ce komai ba bayan fitowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel