Yanzu-yanzu: Kotu a birnin Landan ta hana Ike Ekweremadu beli, tace a garkameshi a Kurkuku
Landan - Kotun kasar Birtaniya dake Landan ta hana tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice, beli.
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kotun ta bada umurnin a garkamesu a magarkama, rahoton AriseNews.
Ike Ekweremadu tare da matarsa sun gurfana yau Alhamis gaban kotun majistaren Uxbridge.

Asali: Original
An damke Sanata Ekweremadu da matarsa kan yunkurin satar sashen jikin wani yaro
Hukumomi a kasar Birtaniya ta damke tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, da matarsa Beatrice kan laifin kai wani yaro kasar don cire wani sashen jikinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar yan sandan kasar ta tabbatar da labarin cewa an garkamesu a kurkuku kuma za'a gurfanar da su a kotu ranar Alhamis bayan gudanar da bincike, rahoton Skynews.

Kara karanta wannan
Har yanzu ban samu wata sanarwa a hukumance daga ubangidana ba - Hadimin Ekweremadu
Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da bincike ne bayan sanar da su wasu sun kawo dan wani kasar kuma hakan ya sabawa dokar bautar zamani na Birtaniya.
Asali: Legit.ng