Shirin 2023: PDP ta shirya a Abuja, ta fara tantance ‘yan takarar mataimakin gwamna

Shirin 2023: PDP ta shirya a Abuja, ta fara tantance ‘yan takarar mataimakin gwamna

  • Tuni jam'iyyar PDP ta fara aikin tantance 'yan takarar mataimakin gwamna a jihohi a babban birnin tarayya Abuja
  • Jihar Akwa Ibom ta samar mace ta farko a matsayin 'yar takarar mataimakin gwamna, an kuma tantance ta
  • Hakazalika dan takarar gwamnan jihar Legas a PDP ya bayyana goyon bayansa ga mutane biyar da ke neman kujerar takara dashi

Abuja - Premium Times ta rahoto cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne jam’iyyar PDP ta fara tantance wadanda za su yi takarar mataimakan gwamna a zaben 2023 mai zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an gudanar da tantancewar ne a hedikwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.

An fara tantance 'yan takarar mataimakin gwamna
Shirin 2023: PDP ta fara tantance ‘yan takarar mataimakin gwamna na jihohi | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kwamitin tantance ‘yan takarar mataimakin gwamna karkashin jagorancin tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Okwesilieze Nwodo, tare da Akilu Indabawa a matsayin sakatare da Sunday Omobo a matsayin sakataren gudanarwa.

Kara karanta wannan

Atiku ya tura manya su yi wa Wike danniyar kirji domin gudun a samu cikas a 2023

Ma ce 'yar takarar mataimakin gwamna ta farko a Akwa Ibom

Wata 'yar takarar mataimakin gwamnan jihar Akwa-Ibom, Akon Eyakenyi, da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan tantance ta, ta yabawa gwamnan jihar da uwargidansa da shugabannin jam’iyyar da kuma al’ummar jihar bisa zabo ta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ms Eyakenyi, ‘yar majalisar dattawa mai wakiltar Akwa-Ibom ta Kudu, wadda kungiyoyin mata daga jihar suka taya murna, ta bayyana cewa matan jihar suna da hakki na jin dadi kan kujerar mataimakin gwamnan da aka ba su a karon farko.

A cewarta:

“Zan je can a matsayina na uwa ga kananan hukumomi 31 na jihar Akwa Ibom da suka kunshi mata da maza da matasa da kuma tsofaffi.
“Zan je can ne domin in yi hidima, domin in ba da misali da tabbatar da cewa a bayana wata mace za ta iya karbar mukamin.

Kara karanta wannan

Poly Bauchi: Babbar ma'aikaciya ta rasa aikinta bisa shiga siyasa da tallata su Tinubu

“Zan kuma tabbatar da cewa mata sun samu hakkinsu a matakin zartarwa, majalisa da jam’iyya.
"Zan kuma zama abin koyi kuma zan zama abin yabo ga kowace mace a jihar Akwa-Ibom."

Mataimaki daga jihar Legas

Dan takarar gwamnan jihar Legas a karkashin jam’iyyar PDP, Olajide Adediran, wanda shi ma a sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa, ya zanta da ‘yan jarida kan wanda zai iya zama abokin gaminsa, rahoton Daily Sun.

Mista Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ya ce zabo mutane biyar domin a zabi daya ya zama abokin takararsa ya nuna cewa Legas cibiya ce mai mutane da dama da suka cancanci wannan matsayi.

A cewarsa:

"Kowane daya daga cikin biyar da aka zaba ya cancanci zama mataimakin gwamna na."

Ya ba da tabbacin cewa abokin takararsa zai yi farin jini fiye da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.