2023: Makomar 'Dan Takarar APC, Bola Tinubu a Jihohi 19 na Arewacin Najeriya
- Batun makomar Tinubu babban abin dubi ne musamman idan aka kalli yadda jam’iyyar APC ta mamaye arewacin Najeriya, yanzu haka ita ke mulkar jihohi 14 cikin 19 da ke yankin
- Sai dai wannan ne karo na farko da jam’iyyar ta gabatar da dan kudu, Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa kuma shi ne zai kara da Atiku da Kwankwaso
- Ganin yadda 'dan takarar ya dinga kaiwa da kawowa a arewacin Najeriya kafin ya bayyana burinsa, ya dinga yada zaman lafiya da hadin kai, ya samu karbuwa a wurin masu zabe?
Menene makomar dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a jihohin arewa yayin zaben 2023 da ke karatowa?
Wannan tambayar ta kunno kai ne daga masu kula da siyasa da kuma kiyasi da hasashe musamman idan aka kalli yadda jam’iyya mai mulkin ce ta fi karfi a yankin arewa don tana shugabantar jihohi 14 cikin 19.
Idan an kula, wannan ne karo na farko da jam’iyyar ta tsayar da dan takarar shugaban kasarta daga yankin kudu.
Tinubu, wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne, ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar da kuri’u 1,271 bayan an yi zaben a ranar 8 ga watan Yuni yayin da ya kayar da ‘yan takara 13, 7 kuma su ka janye tare da mara masa baya a filin zaben.
A ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 ake sa ran za karawa tare da sauran ‘yan takara na jam’iyyu 16, ciki har da na PDP, Atiku Abubakar, na NNPP, Rabiu Kwankwaso da na LP, Peter Obi.
Mai Hakuri, Mawadaci
Kafin bayyanar batun kudirinsa na takara, a watan Janairu Tinubu ne shugaban jam’iyyar APC na yankin Kudu maso yamma kuma tun 1999 yana da rinjaye a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin arewa ne su ka mara masa baya har ya samu nasarar lashe zaben fid da gwanin jam’iyyar. Amma wannan ba abin mamaki bane kasancewar dama Tinubu ya ginu a yankin.
Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru, wanda ya marawa Tinubu baya ta hanyar hakura da takarar ya bayyana yadda Tinubu ya taimaka masa lokacin da ya ke takarar gwamnan jiharsa.
Yadda ya dinga tuntubar gwamnonin arewa
Sai da Tinubu ya tuntubi manyan arewa da dama sannan ya tsaya takara. Tun shekarar da ta gabata Tinubu ya yi ta kai ziyara jihohin arewa kamar Kaduna, Kano da Katsina. Sannan ya tallafawa ‘yan kasuwar Katsina da gobara ta ritsa da su da N50,000 a ranar 24 ga watan Maris din 2021.
Lakcar da yayi a Arewa House
A yayin jawabi a bude taron lakcar Arewa House wanda ya jagoranta a jihar Kaduna awatan Maris din 2021, Tinubu ya yi kira kan saka hannayen jari a wurin samar da aikin yi domin shawo kan matsalar tattalin arziki da kalubalen tsaro a arewacin Najeriya.
Yace dole ne gwamnati ta dinga hangen nesa wurin samo mafita ga kalubalen rashin aikin yi. Kamar yadda yace, fusata da zakuwar matasa wadanda talauci ne silar yasa laifuka suka yawaita.
Lakcar zagayowar ranar haihuwarsa da aka yi a Kano
A taron., wanda ya kaddamar da cibiyar yaki da rashawa ta jihar, Tinubu ya jinjinawa Gwamna Abdullahi Ganduje kan yadda ya karfafa yaki da rashawa a jihar.
Ya yi kira ga zaman lafiya, hadin kai da hakuri da juna a tsakanin 'yan Najeriya kuma ya yi ganawar sirri da malamai da kuma sarakunan jihar masu daraja ta farko a gidan gwamnatin jihar.
Babu shakka wadannan abubuwan suna daga cikin abubuwan da suka bada gudumawa ga tsohon gwamnan Legas din har ya samu goyon baya da gwamnonin Arewacin Najeriya a zaben fidda gwani na APC.
A yanzu da yake 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar, ya yi duk abinda ya dace domin samun alaka mai karfi da masu zabe a yankin?
Habu Muhammad, tsohon shugaban cibiyar bincike da horarwa ta damokaradiyya a jami'ar Bayero dake Kano, yace Tinubu ya ziyarci jihohin arewa maso yamma ne domin daga burinsa na gaje kujerar Buhari a zaben 2023.
Lawan ya tsallake rijiya da baya, sunansa ya maye gurbin na Machina a matsayin dan takarar sanata na APC
Yace da zagayawar da Tinubu yayi a jihohin arewacin Najeriya yayi su ne domin yada hadin kai da zaman lafiya, da ya fara tattara shugabannin kudancin kasar nan kuma ya yada wannan manufar.
Asali: Legit.ng