Yanzu-Yanzu: Na damu da yadda Sanatoci ke ficewa daga jam'iyyar APC, Adamu
- Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce al'adar siyasa ce a irin lokacin da ake fuskantar zaɓe mutane su yi ta sauya sheka
- Ya ce a matsayinsa na shugaba ya shiga damuwa ba kaɗan ba, amma shi da abokan aikinsa na NWC sun shirya shawo kan matsalar
- A yan kwanakin nan, Sanatocin APC kusan 7 ne suka tattara kayansu, suka fice daga jam'iyyar zuwa wasu jam'iyyun hamayya
Abuja - Shugaban jam'iyyar All Progressive Congress wato APC, Sanata Abdullahi Adamu ya nuna damuwa kan yadda guguwar sauya sheka ta mamaye jam'iyya mai mulki.
Daily Trust ta ruwaito cewa Sanatocin APC 7 ne suka sauya sheƙa zuwa wasu jam'iyyun adawa bayan gaza samun tikitin takara a babban zaɓen 2023 da ke tafe.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawar sirri da Sanatocin APC, Sanata Adamu ya ce abin takaici ne yadda yan majalisun ke barin jam'iyya mai mulki.
Ya ce dama ana tsammanin haka kasancewar yanzu ne ake ta shirye-shirye zaɓe, kuma an saba ganin irin haka na faruwa a ƙasar nan a wannan lokacin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaban APC ya ce:
"A duk shekarar zaɓe, irin haka na faruwa da mutane, masu ruwa da tsaki su shiga damuwa. Najeriya ba wata shaffafa da mai bace da hakan zata ƙi faruwa, haka ma APC."
"Sabida haka ba abin da ya shafe ni da kome ke faruwa a sauran jam'iyyu, na jam'iyyar mu ne yake damuna. Kun san cewa ba a APC kaɗai haka ke faruwa ba, saboda muna tsagin jam'iyya mai mulki, matsalar mu ta fi jan hankalin mutane."
Mun damu, amma zamu ɗauki mataki - Adamu
Adamu ya ƙara da cewa abubuwan da ke faruwa na sauya sheka a jam'iyya mai mulki ya sa shi cikin damuwa sosai a matsayinsa na shugaba.
"Babu shugaban da ba zai shiga damuwa idan ya rasa mamba ɗaya ba, ba wai biyu ko uku ba, ɗaya kacal."
"A halin yanzun muna tsakiyar fuskantar damuwar ne amma ni da sauran mambobin kwamitin ayyuka mun shirya fuskantar matsalar kuma zamu warware ta idan Allah ya so."
A wani labarin kuma Sabon rikici ya ɓalle a gwamnatin Kano, Hadimin Ganduje ya zargi kwamandan Hisbah
Wani rikici ya kunno kai tsakanin jami'an gwamnatin jihar Kano kan wasu kujerun hajji da aka ware wa hukumar Hisbah.
Hadimin Ganduje, Mujittaba Rabiu Baban Usman, ya zargi Sheikh Ibn Sina da raba wa iyalansa wasu kujerun gwamnati.
Asali: Legit.ng