Jam'iyyar PDP ta shiga tsaka mai wuya ana gab da zaɓe, Mambobi sama da 500 sun koma APC
- Yayin da ake shirin zaɓen gwamnan Osun a wata mai kamawa, babbar jam'iyyar hamayya PDP ta yi rashin ɗaruruwan mambobinta a Osun
- Sama da mutum 500 suka tabbatar da sauya sheka daga PDP zuwa APC a wurin taron yaƙin neman zaɓen gwamna Oyetola a mahaifarsa
- Gwamna Oyetola ya tabbatarwa mutanen jihar Osun cewa idan suka sake zaɓen sa karo na biyu zasu sha romon demokaraɗiyya
Osun - Mambobin babbar jam'iyyar hamayya PDP sama da 500 daga yankin ƙaramar hukumar Boripe, jihar Osun sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
Jaridar Punch ta rahoto cewa APC ta karbi masu sauya shekan ne a wurin gangamin yaƙin neman zaɓe wanda ya gudana a Iragbiji, mahaifar gwamnan Osun, Adegboyega Oyetola.
Wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na gwamnan Osun, Ismail Omipidan, wacce ya fitar ranar Talata, ta ce mutanen sun ce hanyar da gwamna ke bi wajen tafiyar da harkokin jiha ne ya ja hankalin su.
Haka nan kuma tsofaffin mambobin PDP sun sha alwashin goyon bayan gwamna Oyetola tare da kaɗa masa kuri'un su a zaɓen gwamnan da ke tafe ranar 16 ga watan Yuli, 2022.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Abin da zan yi idan na zarce - Gwamna Oyetola
Da yake jawabi ga dandazon masoya da suka halarci gangamin, Gwamna Oyetola, ya yaba wa mutane bisa dumbin goyon bayan da suke nuna wa gwamnatinsa.
Ya kuma tabbatar musu da cewa idan suka sake amince masa, zangon mulkinsa na biyu, "Zai fi saka wa mutane da kuma magance matsaloli fiye da zangon farko wanda ya gina tushen kyakkyawan gobe."
Oyetola ya kuma roƙi mazauna jihar waɗan da suka jinkirta karɓo katin zaɓen su da su gaggauta zuwa su amso domin su samu damar sauke nauyin su a zaɓen gwamnan da ke tafe.
Sabuwar matsala ta kunno wa Atiku da Tinubu, Dubbannin mambobin APC, PDP sun canza ɗan takarar da zasu zaɓa a 2023
A wani labarin kuma Kotu ta yanke wa matashiyar da ta kashe mahaifiyar tsohon gwamna hukunci
Bayan kama ta da laifin kisan kai, Kotu ta yanke wa yar aikin marigayya mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Edo hukuncin kisa.
Alƙalin Kotun ya ce hujjojin da aka gabatar masa ya tabbatar da cewa yar aikin ce ta kashe uwar ɗakinta Madam Igbinedion.
Asali: Legit.ng