Bayan Tinubu ya lashe zaben, Shugaba Buhari ya faɗi ɗan takarar da yake goyon bayan ya gaje shi a 2023
- Shugaban kasa, Alhaji Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ko a baya ya so ayyana Tinubu a matsayin magajinsa na APC
- Ya ce a yanzun bayan ya lashe zaɓen fidda gwani, zai ba shi cikakken goyon baya har ya samu nasara a babban zaɓe
- Wannan na zuwa ne kusan mako biyu da Tinubu ya lallasa abokan takara a zaɓen fitar da ɗan takara da ya gudana a Eagle Square
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ayyana cikakken goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban kasa da jam'iyyar APC ta zaɓa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Wannan na ƙunshe ne a rubutattun amsoshin tambayoyin da jaridar Bloomberg News ta yi wa shugaban a wata tattaunawa.
Leadership ta rahoto cewa Da aka tambaye shi ko ya yi shirin nuna goyon bayansa ga wani ɗan takara da ya fi so ya gaje shi, idan haka ne to waye? shugaban ƙasa ya ba da amsa da cewa:
"Eh ina da shi, zan goyi bayan ɗan takarar da APC ta tsayar ya gaji kujerar shugaban ƙasa."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Buhari ya kare gwamnan CBN da ya so shiga takara
Haka nan kuma a kokarin kare gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emiefele, bisa yunkurin shiga tseren takarar shugaban kasa, Buhari, ya ce gwamnan ya sha fama da suka.
Hakan ta faru ne saboda a matsayin gwamnan Banki Lamba ɗaya a Najeriya yana da wata rayuwar a wajen abubuwan da suka shafi tattalin arziki, a cewar Buhari.
Buhari ya ce:
"Shugaban ƙasa ke da ikon naɗa gwamnan CBN, amma naɗinsa zai tabbata ne da amincewar majalisar dattawa. Haka nan kuma Daraktocin CBN ne ke ikon yanke ko ayyukan gwamnan sun saɓa doka don tabbatar da ya sauke nauyin dake kansa."
"Amma da akwai wasu zargi da aka masa saboda yana bin wasu hanyoyin wajen aikinsa, an masa laƙabin ɗan siyasa ne. Amma lokaci ya nuna ba haka bane."
"Maimakon haka gwamnan ya na bin duk wani zaɓi da ya samu na haɓaka tattalin arziki da zai jawo mutane ciki su amfana. Ya kamata Najeriya ta zama mai ikon zaɓar hanyar cigaba da gina tattalin arzikinta."
A wani labarin kuma yayin da jita-jita ta yawaita kan mataimakin Tinubu, shugaban APC ya ce suna sane kuma suna bin doka wajen yin komai
Abdullahi Adamu ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da APC ba su taka kowace doka ba yayin miƙa Fom ga INEC.
Bola Ahmed Tinubu ya mika Fom tare da sunan Kabiru Masari a matsayin mataimakin riko kafin a zaɓo na gaske.
Asali: Legit.ng