Kowa da gwaninsa: Inyamurai mazauna arewa sun sha alwashin zabar dan takarar shugaban kasa na APGA a 2023

Kowa da gwaninsa: Inyamurai mazauna arewa sun sha alwashin zabar dan takarar shugaban kasa na APGA a 2023

  • Kungiyar yan kabilar Igbo mazauna jihohin arewa 19 sun bayyana cewa su jam'iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA) za su yi a zaben shugaban kasa na 2023
  • Sun jadadda goyon bayansu ga takarar Farfesa Peter Umeadi da abokin tafiyarsa Abdullahi Mohammed Koli
  • A cewar kungiyar, Umeadi ne ya fi cancanta a cikin dukkanin yan kabilar Igbo da suka fito neman kujerar Buhari

Abuja - Gabannin babban zaben 2023, shugabannin kungiyar Inyamurai ta ‘Ezendi Igbo N’uzo Ije’ a fadin jihohin arewa 19 sun nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA), Farfesa Peter Umeadi.

Shugaban kungiyar, Igwe Ikechukwu Akpudo, ya bayyana cewa suna bayan takarar Umeadi da abokin takararsa Abdullahi Mohammed Koli dari bisa dari, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zulum ne ya fi cancanta ya zama abokin takarar Tinubu, in ji kungiyar masu ruwa da tsaki na APC

Yan Igbo
Kowa da gwaninsa: Inyamurai mazauna arewa sun sha alwashin zabar dan takarar shugaban kasa na APGA a 2023 Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Kungiyar bayan taronta da ta gudanar a Abuja a ranar Juma’a, ta kuma bayyana cewa Farfesa Umeadi ne ya fi cancanta cikin dukkanin yan takarar shugaban kasa daga kabilar Igbo kuma yana da abubuwan da ake bukata a wajen shugaban kasar Najeriya.

Daily Trust ta rahoto cewa Umeadi ya kuma bukaci sarakunan gargajiya na kabilar Igbo a jihohin arewa da su yi aiki tukuru tare da abokin takarar nasa don kawowa jam’iyyar yankin arewa a 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kungiyar ta ce:

“Yan Igbo a jihohin arewa 19 suna maraba da jinjinawa dan takarar shugaban kasa na APGA, dan Anambra, babban alkalin jihar Anambra, Farfesa Peter Umeadi. Muna kuma yaba masa kan tuntubar da ya yi wanda har ya zarce yankin Kudu maso Gabas ya isa ga shugabannin Arewa da sauran shiyyoyin Najeriya.
“Muna baka tabbacin samun goyon baya da kuri’unmu. Haka muna tabbatarwa da iyalan APGA cikakken goyon bayanmu kan sabuwar Najeriya karkashin shugabancinta a zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa."

Kara karanta wannan

Dangin gwamna: Muhimman abubuwa 8 da baku sani ba game da abokin takarar Tinubu

A martaninsa, Umeadi ya nuna godiya ga dattawan kan mara masa baya da suka yi sannan ya dauki alkawarin cewa ba zai taba basu kunya ba.

Ya ce:

“Na yi farin ciki da yadda kuka taru domin bayyana goyon bayanku ga APGA a matsayin jam’iyyar siyasa da kuma takarata gabanin babban zaben 2023. Ina godiya gareku ku dukka.
“Ga abokin takarana, Kwamrad Abdullahi Mohammed Kolo, ina jin dadin aiki tare da kai. Kai dan siyasa ne mai baiwa kuma yarda da kayi ka zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na APGA babban kadara ce ga jam’iyyar da kuma damarta na lashe zabe.”

Ba dai a 2023 ba: Babangida Aliyu ya sha Peter Obi, ya ce ba zai yi mulki ba sai 2027 ko 2031

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu ya bayyana cewa ba lallai ne yan Najeriya sun shirya zabar Peter Obi a matsayin shugaban kasa ba a 2023.

Kara karanta wannan

Muna bukatar PDP ta koma mulki a 2023: Abokin tafiyar Atiku ya lashi takobi

Aliyu wanda ya kasance babban jigo na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana hakan ne a wata hira da gidal talbijin na Channels.

Ya kuma bayyana cewa mutane da dama a jam’iyyar PDP na ta kamun kafa don Obi ya zama mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel