Dalilin da Yasa Atiku Ya Gujewa Wike, Ya Zabi Okowa Mataimakinsa a Takarar Zaben 2023

Dalilin da Yasa Atiku Ya Gujewa Wike, Ya Zabi Okowa Mataimakinsa a Takarar Zaben 2023

  • Bayanai sun tabbatar da cewa, Atiku ya ki daukan Wike matsayin mataimakinsa ne saboda ya zargi cewa Wike baya kaunarsa ko kadan
  • Atiku ya sake shan jinin jikinsa ne bayan da Wike ya koma jihar Ribas bayan zaben fidda gwani kuma ya dinga sukar gwamnonin da suka goyi bayansa
  • An gano cewa, Atiku yayi wa Wike tayin mukami a ma'aikatar man fetur ko wani makusancinsa idan yaci zabe, amma yace sam yafi son ya kasance mataimakin shugaban kasa

Bayanai sun kara bayyana kan dalilin da yasa 'dan takarar shugabancin kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi watsi da mika masa sunan gwamnan Ribas, Nyesom Wike da aka yi kan ya zama abokin tafiyarsa a zaben 2023.

Atiku a ranar Alhamis ya gabatar da gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin wanda ya zaba su yi tafiyar tare, kwanaki 18 bayan tsohon mataimakin shugaban kasar ya ci zaben fidda gwani na 'dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP, karo na biyu a jere.

Kara karanta wannan

2023: Jerin abubuwa 5 da su ka jawo Atiku ya ki daukar Wike, ya zabi Okowa a PDP

Wike, wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwanin, yana daya daga cikin gwamnoni uku da 'yan kwamitin wucin-gadi na PDP suka bukaci Atiku ya duba a matsayin abokin tafiyarsa. Sauran su ne Okowa da takwaransa na Akwa Ibom, Gwamna Udom Emmanuel.

Sai dai, Atiku ya sanar da manyan shugabannin jam'iyyar cewa ba zai iya aiki da Wike ba. Baya ga kwatanta shi da yayi da abokin hamayya na kai tsaye, 'dan takarar yace Wike ba ya kaunarsa inda ya buga misali da yadda ya kusa hana shi cin zaben fidda gwani a 2018 a Fatakwal.

A wannan lokacin, Wike na goyon bayan gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, wanda daga bisani ya zo na biyu a zaben, Premium Times ta ruwaito.

A takaice dai, janyewar da Tambuwal yayi tare da bukatar magoya bayansa da su zabi Atiku suna daga cikin dalilan nasarar Atiku a zaben fidda gwanin da aka yi a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa na Darzo Okowa A Matsayin Abokin Takarata a 2023, Atiku Abubakar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan taron, Atiku ya ziyarci Wike a gidansa dake Abuja, inda gwamnan yayi wa 'dan takarar alkawarin goyon bayansa da jam'iyyar a zabe mai zuwa.

Kamar yadda na cikin gida a jam'iyyar ya bayyana, "Atiku ya firgita bayan Wike ya koma Fatakwal kuma a bayyane ya dinga caccakar takwarorinsa gwamnoni kan goyon bayan Atiku a zaben fidda gwanin."

Atiku ya kara sakankancewa, rikicin da ya shiga tsakanin tsohon shugaban jam'iyyar, Uche Secondus da Wike, ya biyo bayan zargin da gwamnan yayi cewa Secondus na bayan Atiku.

Kamar yadda majiya tace, dattawa da shugabannin jam'iyyar sun ji tsoron zaben Wike saboda zai tarwatsa jam'iyyar a maimakon hada kanta, inda suka ce da yawa daga takwarorinsa na kudu kudu da kudu maso gabas ba su son yadda yake gudanar da lamurransa.

"Shugabanninmu sun shaida rawar da Wike ya taka wurin farfado da jam'iyyar a yayin da take cikin wani hali, amma ba su son yadda yake takama da kuma yadda yake barazana ga jam'iyyar da shugabannin ta a kowanne lokaci.

Kara karanta wannan

2023: Ba A Ga Wike Ba A Wurin Taron Gabatar Da Okowa A Matsayin Mataimakin Atiku

"Sun yarda cewa irin wannan fitinannen ba zai dace da mukamin mataimakin shugaban kasa ba, hakan ne dalilin da yasa shugabannin jam'iyyar ba su goyon bayan Wike," majiyar tace.

Sakamakon karfin da Wike ya nuna a zaben fidda gwani wanda ya janyo masa goyon baya daga deliget a fadin kasar nan, magoya bayansa da shugabannin jam'iyyar suka yi kira ga Atiku da ya dauka Wike a matsayin mataimaki a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 mai zuwa.

An gano cewa, Atiku ya sha alwashin duba Okowa domin ya zama mataimakinsa don ya samu kuri'un deliget din Delta tun a wurin zaben fidda gwani.

Sai dai, bayan ana ta kira ga Atiku a jam'iyyar da ya dauka Wike, ya yi alkawarin bai wa gwamnan Ribas din ko wanda ya zaba matsayi a ma'aikatar man fetur idan ya ci zabe, sai dai gwamnan yayi watsi da hakan. Domin gujewa zargin cewa a 2019 kai tsaye ya zabi Obi, Atiku ya mika lamarin ga shugabannin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar ya Zabi Gwamna Okowa a Matsayin Abokin Tafiyarsa

Duk da kwamitin sun zabi Wike, Atiku ya yanke hukuncin samun Wike ya sanar masa hukuncinsa amma bayan Wike ya gano Okowa Atiku ke so, ya bar garin Abuja da gaggawa.

Har yanzu dai babu tabbacin ko Atiku da Wike sun kara magana bayan Atiku ya sanar da Ifeanyi Okowa matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng