Kuri'arku 'yancinku: Sheikh Gumi ya yanki katin zabe, ya ba 'yan Najeriya shawara

Kuri'arku 'yancinku: Sheikh Gumi ya yanki katin zabe, ya ba 'yan Najeriya shawara

  • Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana a filin rajistar katin zabe, ya inganta katinsa da ya bata
  • Malamin ne ya bayyana hakan a wani rubutu da hoto da ya yada a shafinsa na Facebook a yau Litinin 20 ga watan Yuni
  • Ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su gaggauta samun damar yin katin zabe domin kada kuri'a a zaben 2023 mai zuwa

Kaduna - Shahararren malamin addinin musuluncin nan dake zaune a Kaduna, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Gumi, a ranar Litinin, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yanki katin zabe gabanin 2023 domin sauya tarihin Najeriya.

Malamin ya yi gargadin cewa babu wanda ya isa ya yi korafin rashin gudanar da mulkin adalci idan har bai kada kuri’a a zabe mai zuwa ba.

Kara karanta wannan

Shehin Malamin Musulunci ya yi magana game da hadarin kin mallakar katin zabe

Gumi ya magantu kan batun zabe
Kuri'arku 'yancinku: Sheikh Gumi ya yanki katin zabe, ya ba 'yan Najeriya shawara | Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, Premium Times
Asali: Facebook

Gumi, wanda ya bayyana hakan a shafin sa na Facebook bayan inganta rajistar katin zabensa da ya bata, ya kuma bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta tsawaita atisayen rajistar a yankunan karkara da kuma ‘yan gudun hijira.

Gumi ya ci gaba da cewa babu wani dan Najeriya da ya cancanta ya kada kuri'a da za a tauyewa hakki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shahararren malamin ya rubuta cewa:

“Alhamdulillahi yanzu na inganta rijistar katin zabe na da ya bata.
“Yayin da ya rage kwanaki goma, ina fatan I. N. E. C za ta sake duba batun tsawaita rajistar musamman a yankunan karkara da ‘yan gudun hijira. Duk wani dan Najeriya da ya cancanta bai kamata a tauye hakkinsa ba gwargwadon iko.
“Kuri’ar ku ita ce 'yancin ku na canza lamurra. Idan kun ki kada kuri'a, to, kada ku kara kokawa ga kowa. Allah ya tsare mu baki daya. Amin."

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

Ba ku da tsari: Dan kashenin Jonathan ya fice daga PDP, ya caccaki tsarin jam'iyyar na 2023

A wani labarin na daban, tsohon ministan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Godsday Orubebe, ya yi murabus daga jam'iyyar PDP mai adawa.

Tsohon ministan ya bayyana matakin nasa ne a wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu.

The Cable ta ruwaito cewa Orubebe ya ce murabus din nasa ya fara tun lokacin fitar da wasikar ficewarsa, inda ya kara da cewa shugaban gundumarsa na karamar hukumar Burutu ta jihar Delta yana sane da matakin da ya dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.