Jam'iyyar APC ta Lashe Zaben Gwamnan Ekiti, Ta Lallasa Sauran Jam'iyyu a LGAs 15 Daga Cikin 16
- Jam'iyyar APC ta yi nasarar lashe zaben gwamnan jihar Ekiti da ya gudana a ranar 18 ga watan Yuni inda ta allasa abokan adawa
- Kamar yadda baturen zaben, Kayode Oyebode ya sanar, Biodun Oyebanji na APC ya lashe zaben a kananan hukumomi 15 daga cikin 16 na jihar
- Ya samu jimillar kuri'u 187,057 inda ya lallasa Segun Oni na jam'iyyar SDP wanda ya samu kuri'u 82,211 da Bisi Kolawole na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 67,457
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Ekiti - Biodun Oyebanji, tsohon sakataren gwamnatin jihar Ekiti, ya tabbata wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti.
Kayode Oyebode, baturen zaben da aka yi a ranar Asabar, ya sanar da sakamakon zaben a sa'o'in farko na ranar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.
Oyebanji ya samu kuri'u 187,057 inda ya lallasa manyan masu kalubalantarsa, Segun Oni na jam'iyyar SDP wanda ya samu kuri'u 82,211 da Bisi Kolawole na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 67,457.
Fafesa Kayode Oyebode, baturen zaben, ya bayyana Oyebanji a matsayin wanda yayi nasarar lashe zaben a wurin karfe 3:04 na safiyar Lahadi.
Jimillar 'yan takara 16 ne aka samu suka yi takarar kujerar gwamnan. An samu kuri'u masu amfani 351,865, kuri'u da suka lalace 8,888 sai jimillar kuri'un da aka kada sun kai 360,753.
Ga sakamakon karashe na zaben:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A: 166
AAC: 409
ADC: 5,597
ADP: 3,495
APC: 187,057
APGA: 376
APM: 290
APP: 1,980
LP: 195
NNPP: 529
NRM:347
PDP: 67,457
PRP: 856
SDP: 82,211
YPP: 618
ZLP: 282
APC ta Lashe Zabe a Karamar Hukuma ta Farko a Ekiti
Jam'iyyar APC mai mulki ta tabbata wacce ta lashe zaben gwamna jihar Ekiti da ake yi na karamar hukumar Ikere ta jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Kamar yadda sakamakon da aka sanar ya bayyana daga cibiyar tattara sakamakon zaben, Abiodun Oyebanji na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 12,086, 'dan takarar jam'iyyar PDP, Bisi Kolawole ne ke biye da shi wanda ya samu kuri'u 3,789 yayin a Segun Oni na jam'iyyar SDP ya samu kuri'u 1,934.
Asali: Legit.ng