Ekiti 2020: 'APC N10k, PDP N5k, SDP N3k', - Yar Takarar Gwamna Na ADP Ta Yi Zargin Ana Siyan Kuri'u

Ekiti 2020: 'APC N10k, PDP N5k, SDP N3k', - Yar Takarar Gwamna Na ADP Ta Yi Zargin Ana Siyan Kuri'u

  • Yar takarar gwamna na jam'iyyar ADP, Kemi Elebute-Halle ta zargi jam'iyyun APC, PDP da SDP da siyan kuri'un masu zabe
  • Elebute-Halle ta ce an sanar da ita cewa APC na biyan N10,000, PDP kuma N5000 sannan jam'iyyar SDP na biyan masu zabe N3,000
  • Yar takarar gwamnan ta ce ta yi imanin cewa duniya na kallo kuma mutanen Ekiti za su zabi wanda ya cancanta duk da kudin da ake basu na siyan kuri'u

Ekiti - Kemi Elebute-Halle, yar takarar gwamna na jam'iyyar Action Democratic Party (ADP) a jihar Ekiti, ta yi ikirarin cewa wasu jam'iyyan siyasa suna siyan kuri'un masu zabe a zaben da ke gudana a yanzu.

Elebute-Halle ta yi magana da The Cable bayan ta jefa kuri'arta a rumfa na takwas, gunduma ta 10 a karamar hukumar Ikole a Ekiti.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Ekiti: Mazauna Jihar Sun Bayyana Wadanda Za Su Zaba

Kemi Elebute-Halle, yar takarar gwamna na ADP a zaben Ekiti.
Ekiti 2020: 'APC N10k, PDP N5k, SDP N3k', - Yar Takarar ADP Ta Yi Zargin Ana Siyan Kuri'u. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yar takarar gwamnan ta yaba yadda ake tantance mutane da jefa kuri'a a mazabarta tana mai cewa akwai nagarta.

Kemi Elebute-Halle ta ambaci kudin da wasu jam'iyyu ke siyan kuri'u da shi

Ta yi zargin jam'iyyun APC da PDP da SDP suna siyan kuri'un masu zabe da N10,000; N5,000; da N3,000 kamar yadda aka jero jam'iyyun.

Elebute-Halle ta bukaci masu zabe su zabi wanda ya fi cancanta ta tare da la'akari da kudin da jam'iyyun siyasa suka basu ba.

"Kawo yanzu dai komai na tafiya cikin nagarta," in ji ta.
"At rumfar zabe na - gunduma ta 10, rumfa ta 8 - an sanar da mu APC sun fara siyan kuri'u da N10,000; PDP suna siya da N5,000 kuma SDP da N3,000.
"Muna fatan duniya na kallonsu. Wani abu a rayuwa shine duk wani abin da aka boye zai fito.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Na tabbata Zan Yi Nasara, Ba Zan Janye Wa Atiku Ko Tinubu Ba

"Mun yi imani da mutanen mu cewa duk abin da aka basu; za su yi zabe kuma muna fatan canji na gari."

Yan takara 16 ne suka fafatawa a zaben na gwamnan jihar Ekiti a kananan hukumomi 16 na jihar.

Ekiti 2022: 'Idan Ba Kuri'a, Ba Kudi', Bidiyon Tinubu Yana Yi Wa Masu Zabe Ba'a a Wurin Kamfen

A wani rahotn daban, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci al'ummar Jihar Ekiti su fito su yi zabe idan ba hakan ba ba za a biya su ba.

Tinubu, wanda ya ziyarci a Jihar Ekiti a ranar Talata ya furta hakan ne wurin yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam'iyyar, Biodun Oyebanji gabanin zaben da ake shirin yi ranar Asabar 18 ga watan Yunin 2022.

Ya kuma kambama kansa cewa bai taba fadi zabe ba a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164