Musulmi da Musulmi: Shin APC ta yi wa Kiristocin Arewa adalci? daga Muhammad Auwal

Musulmi da Musulmi: Shin APC ta yi wa Kiristocin Arewa adalci? daga Muhammad Auwal

Bayanin Edita: Muhammad Auwal, marubuci ne mai zaman kansa wanda ke zaune a jihar Kaduna, a wannan zauren, ya yi sharhi kan batun da ke ta haddasa cece-kuce a baya-bayan nan game da rade-radin da ake yi cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai zabi Musulmi dan arewa domin su yi takara tare.

Sanin kowa ne jam'iyyun siyasa sun fitar da ƴan takaransu na muƙamai daban daban ta hanyar zaɓukan fidda gwani, amma abinda ake sauraro shi ne sunayen abokan takarar nasu, musamman a matakin shugaban ƙasa da gwamna.

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi lallai akwai shugaban ƙasa da mataimakinsa, don haka dole jam'iyyu su cike guraben nan biyu a tsakanin ƴan takararsu, amma kundin bai fayyace addini ko wata ƙabila ko yanki da ya kamata ƴan takarar su fito ba.

Kara karanta wannan

2023: Sabbin bayanai masu ƙarfi kan wanda PDP ke shirin bayyana wa a matsayin mataimakin Atiku

Bola Ahmed Tinubu
Musulmi da Musulmi: shin APC ta yi wa Kiristocin Arewa adalci? Daga Muhammad Auwal Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP
Asali: Twitter

Sai dai tun 1999 ƴan siyasa da jagorori masu hangen nesa suka tsiri tsarin haɗa Musulmin Arewa da Kiristan kudu a tikiti ɗaya na takarar shugabancin ƙasa don tafiya tare da tabbatar da haɗin kai.

A halin da ake ciki a yanzu, ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar zai zaɓo mataimakinsa daga kudancin Najeriya kuma kirista, wannan bai saɓa ma tsarin da aka saba ba. Amma ɗan takarar APC mai mulki, Ahmed Bola Tinubu ana tunanin ba lallai ya zaɓo Kiristan Arewa ba duba da cewa shi Musulmi ne daga kudancin ƙasar, kuma a wannan gaɓar tirka tirkar take.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tabbas Musulman Arewa sun ninninka kiristocin Arewa yawa, amma duba da halin rashin yarda da juna da ake ciki a yankin sakamakon rikice rikicen addini da na ƙabilanci daya dabaibaye Arewa, abu ne mai kamar wuya Tinubu ya samu goyon bayan Musulman Arewa idan har ya ɗauki Kiristan Arewa a matsayin mataimakinsa.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya fice daga jam'iyya bayan shan kaye a zaɓen fidda gwani

Shi ma Tinubu wannan ne kaɗai dalilin da yasa ba zai kuskura ɗaukan Kiristan Arewa ba. Ta yaya ake tunanin Kiristan Arewa zai kawo ma Tinubu ƙuri'un Kano, Katsina, Borno, Kaduna da Jigawa?

Haka zalika gwamnonin jam'iyyar APC daga yankin Arewa su 14 sun taka rawar gani wajen samun nasarar Tinubu a zaɓen fidda gwani, kuma a irin siyasarmu ta 'ba ni gishiri in baka manda' su ɗinne kuma zasu yi ruwa su yi tsaki wajen taya shi zaɓar mataimaki musamman daga yankin nasu.

A halin da ake ciki jam'iyyar APC na da jahohi 14 a Arewa, 13 daga cikin gwamnonin Musulmai ne, da wani dabara zasu tallata Kiristan Arewa ga ɗimbin Musulman dake jahohinsu har su yarda su zaɓi Tinubu bayarabe da shi Kiristan a matsayin wakilinsu?

Idan aka yi duba da kundin tsarin mulki, yace sai ɗan takarar shugabancin ƙasa ya samu kaso 25 na ƙuri'un da aka kaɗa a jahohi 2 bisa 3 na Najeriya. Anan ana maganan kaso 25 na ƙuri'un aƙalla jahohi 25 kenan.

Kara karanta wannan

2023: Watakila Bola Tinubu ya dauki Musulmi a ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa

A maslahan cin zaɓe na Tinubu, dole sai ɗan mataimakinsa ya zama Musulmi ɗan Arewa ne zai iya samun kaso mafi tsoka daga jahohin Arewa maso yamma da suka haɗa da Kaduna, Kano, Katsina Jigawa, Zamfara, Sakkwato da Kebbi. Kuma su ne jahohin da suka fi yawan ƙuri'u idan ka haɗasu da Borno da Legas, dukkanin jahohi 8 na APC ne!

Haka zalika Arewa maso gabas da ta haɗa da Borno, Yobe, Gombe, Taraba, Adamawa da Bauchi, APC na 3, PDP na da 3, koda yake nan ne yankin Atiku, amma APC za ta samu ƙuri'un da take buƙata.

Arewa ta tsakiya kuwa (Neja, Nassarawa, Kwara, Kogi, Benuwe da Filato) APC na da 5, PDP na da 1, za a iya raba ƙuri'u anan saboda duk da jahohi ne na APC, amma akwai Kiristoci dayawa a yankin wanda zasu ma APC bore.

A yakin kudu maso yamma kuwa, yankin da Tinubu ya fito, akwai jahohi 6, guda 5 APC ke mulka yayin da PDP ke da ɗaya tal! Cinye du Tinubu zai ma ƙuri'un yankin nan sakamakon Yarbawa na ganin lokacinsu na sake ɗarewa karagar shugabancin Najeriya ne, kuma sun fi fifita ƙabilanci akan addini.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Bola Tinubu ya sa labule da gwamnonin arewa 10 kan wanda zai zama mataimaki

Yankin da Atiku ke tinƙaho zasu mara basa kuwa, watau Kudu maso gabas, yankin Inyamurai, suna fama da matsalolin ƴan ta'addan IPOB masu rajin kafa ƙasar Biyafara ta hanyar ɓallewa daga Najeriya, ko a kwanaki sun bindige jami'an INEC dake aikin rajistan katin zaɓe, da ma sauran hare haren da suke kai ma jami'an gwamnati. A yanzu haka ana kwashe kwanaki 2 zuwa 3 ba a fita a yankin, kuma dokar IPOB ne! Wannan kaɗai barazana ce ga kuri'un da Atiku ke sa rai, saboda jama'an yankin ba lallai su fita su yi zaɓe yadda ya kamata ba.

Bugu da ƙari a wannan karon akwai ɗan takara daga yankin, Peter Obi, tsohon gwamnan Anambra, kuma tsohon ɗan takarar mataimakin shugabancin ƙasa na Atiku a 2019, hakan na nufin zai raba ma Atiku kuri'a. Ko a zaɓen 2019 jahohin yankin; Imo, Enugu, Abia, Anambra da Ebonyi, ƙuri'u miliyan 1 suka baiwa Atiku na jam'iyyar PDP. Ita dama jam'iyyar APC ba ta ɗaura a ka ba!

Kara karanta wannan

Rigima bata ƙare ba: Bayan ganawa da Gwamnoni, BoT sun lallaɓa sun sa labule da Atiku kan mataimaki

A yankin Kudu maso kudu kuwa, Atiku zai samu ƙuri'u yadda ya kamata sakamakon gwamnonin yankin banda guda ɗaya (Na Cross Rivers) duk ƴan PDP ne. Amma basu da ƙuri'u dayawa, saboda a 2019 ƙuri'u dubu 500 suka baiwa Atiku, ma'ana ƙuri'un da kudu maso gabas da kudu maso kudu suka baiwa a Atiku tare da Peter Obi a 2019 miliyan 1.5 basu kai abinda APC ta samu a jahar Kano kaɗai ba, balle kuma a yanzu Atiku da Peter sun rabu!

Hakan ke nuna idan ka haɗa jahohin Arewa 19, da na Yarbawa 6 kaɗai Tinubu yaci zaɓe, idan kuma aka haɗa da rarume rarumen ƙuri'un sauran jahohi, nasara ta tabbata kenan, amma fa idan ya zaɓo ƙwararre, jajirtacce, kuma fitaccen Musulmin Arewa kenan.

Saboda haka batun takarar Tinubu a APC tare da mataimaki Musulmi daga Arewa ba batun rashin adalci ga Kiristocin yankin ko ƙyama bane, a'a, illa dai maslaharsa ce kawai na cin zaɓe.

Ku sani: Ra'ayoyi da sharhin da aka yi a nan na marubucin ne kuma ba lallai ba ne sun yi daidai da manufa ko matsayin Legit.ng Hausa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng