Dan takarar shugaban kasa: Mata ta ta so na jika deliget da kudi, na ki, kuma na ci zabe
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Dumebi Kachikwu, ya bayyana yadda ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar
- A cewar Dumebi, matar sa ta roke shi da ya ba deliget na jam’iyyar kudi a kokarin da yake na ganin ya samu tikitin takarar shugaban kasa, amma ya ki amincewa
- Dan takarar wanda kanin tsohon karamin ministan mai ne, Ibe Kachikwu, ya bayyana cewa zai lashe zaben shugaban kasa a 2023
A ranar Laraba, 15 ga watan Yuni, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC kuma shugaban gidan talabijin na Roots TV, Dumebi Kachikwu, ya bayyana cewa matarsa ta roke shi da ya ba da cin hancin deliget a zaben fidda gwanin da aka kammala domin gudun wulakanci.
Ya ce duk da cewa bai kashe wa deliget ko kwabo ba kafin zaben fidda gwanin, amma ya yi mamakin yadda ya kayar da ‘yan takarar da ke raba kudi ga su deliget din.
Kachukwu ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, jaridar Punch ta ruwaito.
Dumebi ya yi magana a kan kiran da ya yi wa daya daga cikin abokan hamayyarsa
Ya kuma ce ya yi kiran waya ba adadi ga daya daga cikin abokan hamayyarsa bai dauka ba kuma bai kira daga baya ba bayan nasarar da ya samu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yace:
“Na hada liyafa ga daukacin deliget, na sanar da su cewa ni mai son yin takara ne amma na ce musu ba ni da kudi, su zabi lamirinsu domin idan na yi nasara, lamirina ya samu ‘yanta cewa ba kudi na biya ba.
“Idan na sha kaye, ina da kasuwancina da zan koma. Don haka ba sai na zama shugaban kasa don yi wa Najeriya hidima ba. A wannan daren na bar su, ban san yadda makoma za ta kasance ba.
“Na sanar da su cewa ba zan ba kowa kudi ba. Wasu sun fusata, na bar su ban san mene ne makoma ta ba. Abokan hamayya na sun raba kudi ga deliget.
"Da safe washegari, matata ta ce, ‘Don Allah ka kashe kudin nan a kan deliget don guje wa wulakanci, kana da shi’ sai na ce mata lamirina ya hana hakan.
"Ina tsammanin an gama, tuni na fara shirya jawabina na yarda da shan kaye sai na ga yanayin jikin deliget ya canza, suna murmushi a gare ni.
“Abin da ya fi zafi shi ne ganin wadanda suka yi asara sun je kafafen yada labarai domin su bata tsarin da ya samar da ni. Karya suke yiwa jama'a.
“Na kira daya daga cikin 'yan takara, ya ce ba ya kusa da Abuja, yana Legas. Na tashi zuwa Legas don ganinsa, tun daga lokacin bai dauki waya ta ba.”
Dumebi yayi magana game da zaben 2023
Ya kuma bayyana fargabarsa kan zaben 2023, inda ya ce kimanin ‘yan Najeriya miliyan 50 da ke matsakaiciyar rayuwa a birane ba sa shiga a dama da su a zabe saboda halin ko-in-kula.
Yayin da yake tabbatar da cewa akwai babban aiki a gabansa, ya ce:
"An shaidi Najeriya da son kai kuma akwai bukatar a canza yadda mutane ke dabi'antuwa, tunani da lissafi."
Ban hakura ba fa: Zan sake tsayawa takarar shugaban kasa, in ji Yahaya Bello
A wani labarin, Channels Tv ta rahoto cewa, gwamnan jihar Kogi kuma dan takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Yahaya Bello, ya ce zai tsaya takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Wannan kenan kamar yadda ya lura cewa burinsa na yin shugabanci a 2023 ya ci tira kuma ya yi "gwajin makirufo ne kawai."
Bello, wanda ya samu kuri’u 47 a zaben da aka gudanar a makon da ya gabata ya bayyana hakan ne ga ‘yan jaridun fadar gwamnatin kasa jim kadan bayan ya gana da shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya).
Asali: Legit.ng