Shirin 2023: PDP ta yi watsi da batun zaban Wike a matsayin abokin takarar Atiku

Shirin 2023: PDP ta yi watsi da batun zaban Wike a matsayin abokin takarar Atiku

  • A dai dai lokacin da ‘yan Najeriya ke jiran a bayyana gwamnan Rivers, Nyesom Wike a matsayin mataimakin Atiku Abubakar, jam’iyyar PDP ta fasa kwai
  • A wani sako daga jam'iyyar a ranar Laraba, 15 ga watan Yuni, sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, Debo ya bayyana cewa ba a zabi Wike ba
  • Ologunagba, ya ce ikirarin cewa an riga an zabi Wike ga tafiyar karya ne domin har yanzu dai ana ta shawari a kai

Abuja - Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi watsi da rade-radin da ake yi cewa kwamitinta ya zabi gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar.

Vanguard ta ruwaito cewa, kwamitin zaben na jam’iyyar PDP, ya yi taro a jiya, domin cika aikin da ya rataya a wuyansa na ba da shawarar kan abokin tafiyar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, watakila a tantance Gwamnan PDP a matsayin Abokin takarar Atiku a 2023

Batun daukar Wike a matsayin mataimakin Tinubu
Shirin 2023: PDP ta yi watsi da rahotannin zaben Wike a matsayin abokin takarar Atiku | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Da yake magana kan wannan lamari a Abuja, Laraba, Sakataren Yada Labarai na kasa na PDP, Debo Ologunagba, ya ce rahotannin da ake yadawa a kafafen yada labarai na cewa PDP ta zabi Wike kawai jita-jita ne.

Ya ce a halin yanzu kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar na duba lamarin tare da tuntubar juna, domin duba wanda ya fi kowa cancanta ya yi takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar a zaben 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A halin da ake ciki, Ologunagba, wanda ya jaddada cewa PDP ta fara gudanar da ayyukanta na tantancewa, ya sanar da cewa za a yi taro a yau Laraba da karfe 11 na safe, inda ya ce ana sa ran za a duba kwamitin da ke shawari kan lamarin.

Shugaban PDP ya bayyana lokacin da za a sanar da abokin tafiyar Atiku

Kara karanta wannan

Abokin tafiyar Atiku: PDP ta rage, tana duba hada Atiku da daya cikin wasu jiga-jigai 3

A wani labarin, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyiochia Ayu, a ranar Talata, ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, a cikin sa’o’i 48 masu zuwa, za su fadi abokin gamin Atiku gabanin zaben 2023.

Ayu ya ba da wannan tabbacin ne a jawabin bude taron da ya yi da mambobin kwamitin tuntuba da aka kafa domin taimakawa Atiku wajen zaben wanda zai yi takara tare dashi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ayu na ganawar sirri da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a sakatariyar jam’iyyar ta kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.