Kwamitin PDP sun zabawa Atiku wanda ya dace ya zama Mataimakinsa a zaben 2023
- ‘Yan kwamitin PDP sun yarda Nyesom Wike ya zama abokin takarar Atiku Abubakar a zaben 2023
- Duk da Gwamna Nyesom Wike shi ne babban wanda ya kalubalanci Atiku, za su tsaya takara tare
- Kwamitin ya karkare aikinsa a wani zama da mataimakin shugaban PDP na kasa ya jagoranta a jiya
Abuja - Idan ba an samu wasu sauyi a mintin karshe ba, Nyesom Wike ne wanda zai yi takara a PDP tare da Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa.
Rahoton da ya fito daga Daily Trust a ranar Talata, 14 ga watan Yuni 2022, ya tabbatar da cewa Gwamna Nyesom Wike ne wanda kwamiti suka zaba.
Kwamitin kasa na musamman da jam’iyyar PDP ta ba alhakin zaben ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 ya bukaci a dauki Gwamnan jihar Ribas.
Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa kwamitin ya amince Nyesom Wike wanda ya zo na biyu a zaben fitar da gwani ya raba tikiti tare da Atiku Abubakar.
Daga bakin wani 'dan kwamitin
“Kwamiti ya zabi Gwamnan Ribas, Nyesom Wike. Ya samu kuri’u masu yawa a wajen ‘yan kwamitin.”
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“’Yan kwamitin su na ganin shi ne wanda ya fi dacewa ya zama abokin takarar Atiku Abubakar a zaben.”
“Kun ga kokarin da ya yi a zaben fitar da ‘dan takarar shugaban kasa. Ana ganin zai iya wannan aiki.”
- Majiya
Wike ya doke takwarorinsa
Rahoton ya ce Nyesom Wike ya samu goyon bayan mutane 16 daga cikin ‘yan kwamitin Janar Aliyu Gusau wanda shi PDP ta daurawa nauyin wannan aiki.
The Cable ta samu labarin a jiya, ta ce mafi yawan 'yan kwamitin sun fi gamsuwa da Atiku a kan Gwamna Ifenayi Okowa da kuma Gwamna Udom Emmanuel.
Wadanda suka halarci taron da Ambasada Umaru Damagun ya jagoranta sun hada da wasu Gwamnoni; Samuel Ortom, Aminu Tambuwal da Bala Mohammed.
Sauran su ne Babangida Aliyu, Liyel Imoke, Olusegun Mimiko da irinsu Hon. Ndudi Elumelu.
SERAP ta jefa kalubale
Dazu mu ka samu labari cewa kungiyar SERAP ta na so duk mai neman zama shugaban kasa ya sanar da mutanen Najeriya nawa yake cikin asusun bankinsa.
Kungiyar ta ke cewa ‘dan takara daya ne kurum ya fadi silar dukiyarsa, amma Asiwaju Bola Tinubu da su Atiku Abubakar ba su bayyana sirrin dukiyarsu ba.
Asali: Legit.ng