Arewa, da jerin kalubale 7 da suke jiran Peter Obi idan ya shiga takarar Shugaban kasa
- Peter Obi yana cikin ‘yan gaba-gaba a wajen neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023
- ‘Dan takaran na Jam’iyyar LP ya samu karbuwa musamman a wajen matasan kudancin Najeriya
- Amma hakan bai nufin zai ci karo da wasu matsaloli a babban zaben da za ayi a shekara mai zuwa
Legit.ng Hausa ta yi nazarin takarar Peter Obi da yadda za ta iya kayawa da shi a jam’iyyar LP a zaben shekarar 2023.
1. Rashin jam’iyya mai karfi
Babu abin da zai kawowa Peter Obi cikas kamar jam’iyyar da ya tsaya takara (Labor Party). A zaben 2019 ya samu kuri’u tare da Atiku Abubakar saboda ya tsaya takara ne a PDP.
2. LP ba ta da iko da jihohi
Cin zabe a Najeriya yana bukatar mutum ya samu iko da Jihohi saboda tsadar zabe da dawainiyar da ake yi. A halin yanzu jam’iyyarsu Obi ba ta rike da wata jiha a kaf Najeriya.
3. Karancin manyan ‘yan siyasa
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Peter Obi bai da wani babban ‘dan siyasa da yake tare da shi ko ya bi shi zuwa LP. Haka zalika babu wani babban ‘dan siyasa mai mabiya wanda ya shiga jam’iyyar da Obi ya koma.
4. Karfin sauran jam’iyyu a yankinsa
Inda Obi zai gamu da cikas kuma shi ne jam’iyyar PDP ta yi karfi a yankin da ya fito. PDP ta na rike da Enugu da Abia, APC ta na mulki a Ebonyi da Imo, APGA ta kama Anambra.
5. Kafuwa a siyasa
Ba a sa ‘dan takaran shugaban kasar a cikin ‘yan siyasan da suka kafu sosai a kasar nan. Duk da ya yi gwamna na shekaru kusan 8, ana yi wa Obi gori da cewa bai da ta-cewa ko a jiharsa.
6. IPOB
A zaben 2023, ‘yan ta’addan IPOB za su iya kawowa burin Obi cikas. Tsageru su kan hana mutanen Kudu maso gabas fita daga gida, hakan zai yi tasiri a kuri’un da za a samu.
7. Rashin karbuwa a Arewa
'Dan siyasar mai shekara 60 bai da farin-jini a yankin Arewacin Najeriya da aka fi samun kuri’u masu yawa. Ana yi wa Obi zargin cin zarafin mutanen yankin sa’ilin da yake gwamna.
8. Rikicin shari’a
A jerin na mu rikicin cikin gida shi ne cikas na karshe da ‘dan takarar zai iya fama da shi. A halin yanzu mutane kusan uku suke ikirarin su ne asalin ‘yan takaran LP a zabe mai zuwa.
Kalubalen SERAP
A baya an samu labari, kungiyar SERAP ta na so duk mai neman zama shugaban kasa ya sanar da ‘Yan Najeriya nawa yake cikin asusun bankinsa da tarin kadarorinsa.
‘Dan takara daya ne kurum ya fadi silar dukiyarsa, amma Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi da su Rabiu Kwankwaso ba su bayyana sirrin dukiyarsu ba.
Asali: Legit.ng